Dakarun sojin Najeriya sun tarwatsa ma'adanar makaman 'yan ta'adda a Borno, sun bi ta kan wani da motar yaki (Bidiyo)

Dakarun sojin Najeriya sun tarwatsa ma'adanar makaman 'yan ta'adda a Borno, sun bi ta kan wani da motar yaki (Bidiyo)

Farmakin da sojin saman Najeriya karkashin rundunar Operation Lafiya Dole ta kai a Njimia da ke dajin Sambisa, ya tarwatsa kayan yakin 'yan ta'addan Boko Haram.

Hari ta jiragen saman yakin da dakarun suka kai a ranar Talata ya biyo bayan rahotannin sirrin da suka samu a kan makaman 'ya ta'addan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda bayanan suka nuna, wurin adanar makaman na nan a kusa da inda mayakan ke amfani da shi a matsayin sansani. Suna ajiye man fetur da sauran kayayyakin bukata, kamar yadda takardar da Manjo Janar John Enenche ya fitar ta bayyana.

Ya ce babu kuskure harin da suka kai ya samu inda suka saita tare da tashin yankin. A take kuwa ma'adanar makaman suka kurmushe tare da yin mummunar barna ga mazaunin 'yan ta'addan.

A wani bidiyo da dakarun sojin Najeriyan suka fitar, sun fatattaki mayakan ta'addancin har zuwa cikin daji inda suka yi nasarar bi ta kan daya daga ciki da motar yaki.

Kamar yadda biyon ya nuna, tun kafin sojin su tarar da dan ta'addan, ya fadi kasa warwas da alamar harsashi ya samesa kuma ya matukar gajiya.

KU KARANTA: Bude masallatai: Majalisar malaman Kano ta yi zazzafan martani ga Ganduje

A wani labari na daban, majalisar malaman jihar Kano ta ce kamata yayi gwamnati ta yi tunani kafin yanke hukuncin dawo da gabatar da sallar Juma'a da idi a jihar saboda yuwuwar yaduwar cutar korona.

Mallam Ibrahim Khalil, shugaban kungiyar majalisar malaman Kano, ya sanar da BBC cewa gwamnatin jihar ba ta tuntubesu ba a yayin yanke wannan hukuncin nata. Amma ya kamata a ce ta yi la'akari da bukatar jama'a.

Kamar yadda malamin ya bayyana, ya ce ya zama dole a kan gwamnati ta duba damuwar jama'arta da kuma abinda ya dace, tunda bata tuntubi majalisar malamai ba.

A cewarsa, "Amma irin wannan yanayi na annoba da ake ciki, duk wanda yake jin tsoron cewar zai kamu da cutar idan yaje masallacin ko kuma zai zama hadari, to zai iya zamansa a gida."

Amma wanda kuma yake ganin shi zai iya zuwa masallacin ba tare da wata matsala ba, to shi wannan zai iya zuwa masallaci ya yi sallah in ji malamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel