Cakwakiya: Yariya mai shekaru 14 da ubanta ya dirkawa ciki ta haihu a Najeriya

Cakwakiya: Yariya mai shekaru 14 da ubanta ya dirkawa ciki ta haihu a Najeriya

A cikin satin nan da ya gabata ne dai al'ummar garin Abaranj dake a unguwar Ikotun ta jihar Legas suka shiga cikin halin al'ajabi da mamaki yayin da suka samu labarin cewa wata yariya mai shekaru 14 kacal a duniya da uban ta yayi ma ciki ta haihu.

Yarinyar wadda aka sakaya sunan ta dai 'yar aji 3 ce a makarantar karamar Sakandire kuma tun a watan Mayun shekarar da ta gabata ne mahaifin na ta ya dirka mata ciki amma kuma sai ya killace ta a gidan wani mai maganin gargajiya har sai da ta haihu.

Cakwakiya: Yariya mai shekaru 14 da ubanta ya dirkawa ciki ta haihu a Najeriya
Cakwakiya: Yariya mai shekaru 14 da ubanta ya dirkawa ciki ta haihu a Najeriya

KU KARANTA: Hotunan ganawar Buhari da 'yan makarantar Dapchi

Legit.ng ta samu cewa sai dai uban yace lokacin da yayi ta'asar yana cikin maye ne sannan kuma yayi nadamar aikata hakan da yayi sannan kuma ya roki sassafci daga bangaren kotu wajen hukuncin da za'a yanke masa.

A wani labarin kuma, Wata babbar kotu dake zaman ta a garin Kalaba, babban birnin jihar Kuros Ribas a jiya ta yankewa wani tsohon ma'aikacin hukumar rukunin kamfunann NNPC na gwamnatin tarayya mai suna Mista Godwin Elewana hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ita dai kotun ta yanke masa wannan hukuncin ne bayan samun sa da ta yi da laifin kashe wani matashi mai shekaru 22 a duniya mai suna Dougulas Ojugbo bisa zargin sa da yin lalata da diyar sa mai suna Mercy tun a ranar 10 ga watan Maris, shekarar 2015.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng