Shugaba Buhari ya isa jihar Neja, ya kaddamar da sabbin gine-gine
A ziyarar jaje da kai gaisuwa da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi, ya dira a jihar Neja yau Alhamis, 15 ga watan Maris 2018.
Shugaba Buhari ya isa garin inda gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello da mukarrabansa suka tarbesa.
Isarsa ke da wuya, shugaba Buhari ya kaddamar da wani sabon kamfanin Sukari da gwamnatin jihar tayi saboda mazauna jihar.
Daga cikin wadanda suke wajen sune gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, shugaba masana’antar filawa na Najeriya, John G. Coumantaros, da sauransu.
Jiya Buhari ya kai wannan ziyara ne bayan dawowar daga jihar Yobe inda ya kai ziyarar jaje da tabbatarwa gwamnatin jihar da iyayen yan matan Dapchi cewa lallai gwamnati ta shirya ceto yan matan da yan kungiyar Boko Haram suka sace.
KU KARANTA: Matashi ya rataye kansa saboda an ki amincewa ya auri masoyiyarsa a Jigawa
Shugaban kasan dai ya kai ziyara jihar Taraba, sannan ya je Benue, Yobe da kuma jihar Neja yau. Ana sa ran zai tafi jihar RIbas kamar yadda yayi alkawari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng