Na mu ya samu: Dan Najeriya ya zama Sanata a kasar Italiya

Na mu ya samu: Dan Najeriya ya zama Sanata a kasar Italiya

Wani mutum mai suna Toni Iwobi wanda dan asalin kasar Najeriya ne da aka haifa a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya ya samu nasarar zama dan majalisar dattijai a kasar Italiya dake tarayyar turai a zaben da ya gudana.

Shi dai Mista Iwobi kamar yadda muka samu ya tafi kasar ta Italiya ne tun shekara ta 1970 inda kuma ya shiga harkar siyasar kasar kafin daga bisani ya samu mukamin jami'in 'yan kasar waje na jam'iyyar sa.

Na mu ya samu: Dan Najeriya ya zama Sanata a kasar Italiya
Na mu ya samu: Dan Najeriya ya zama Sanata a kasar Italiya

KU KARANTA: Ma'aikata a Filato sun samu hutu dalilin zuwan Buhari

Legit.ng dai ta samu cewa Mista Iwobi din ne ya sanar da samun nasarar ta sa a wani rubutun da yayi ya shelanta a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook inda ya godewa dukkan wadan da suka zabe sa.

A wani labarin kuma, Wata kungiyar matasan jam'iyyar adawa ta kasa watau Concerned Peoples Democratic Party Youths a turance sun fitar da gwamnan jihar Gombe takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar matasan Malam Sani Bello ya fitar dauke da sa hannun sa a jiya Talata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel