Nigerian news All categories All tags
Yanzu Boko Haram ba ta da wani katabus a kasar mu - Shugaba Buhari

Yanzu Boko Haram ba ta da wani katabus a kasar mu - Shugaba Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya Talata ya bayyana cewa kungiyar ta'addancin Boko Haram kawo yanzu ba ta da wani katabus din da za'a rika maganar ta a kasar duk kuwa da sabbin hare-haren da ta kai a makarantar kwana ta 'yan mata a Dapchi da kuma kauyen Rann a jihar Borno a yan kwanakin nan.

Sai dai da ya ke karin haske, shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan hare-haren na ta'addancin babu gwamnatin da ke iya hana yin su dun kuwa da irin tsaron da ke gare ta a kasa.

Yanzu Boko Haram ba ta da wani katabus a kasar mu - Shugaba Buhari

Yanzu Boko Haram ba ta da wani katabus a kasar mu - Shugaba Buhari

KU KARANTA: Duk hassadar 'yan adwa sun san mun yi kokari a fannin tsaro - Buhari

Legit.ng ta samu cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi wannan ikirarin ne a ta bakin mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya wakilce sa a taron masana da masu ruwa da tsaki na bitar kan tsaro karo na takwas da a ka gudanar a garin Abuja.

A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Filato dake a yankin Arewa ta tsakiya ta sanar da bayar da hutu ga dukkan ma'aikatan ta a jihar domin samun damar tarbar shugaba Muhammadu Buhari da zai ziyarci jihar a ranar Alhamis 8 ga watan Maris.

Shugaban ma'aikatan jihar Mistam Izam Azi shine ya sanar da wannan matakin da gwamnatin ta dauka a jiya Talata jim kadan bayan gama wani taron tattaunawa na gaggawa da majalisar zartarwas kasar ta gudanar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel