Canja jadawalin zabe: Jerin Sanataci 10 da zasu sha gudumar majalisa saboda kalaman adawa

Canja jadawalin zabe: Jerin Sanataci 10 da zasu sha gudumar majalisa saboda kalaman adawa

- Majalisar Dattawa zata gudanar da bincike kan wasu Sanatoci goma da ake zargin su da danganta sabon jadawalin zaben da musgunawa shugaba Buhari

- Sanata Dino Melaye na jihar Kogi ne ya karanto kudirin a gaban majalisar inda ya ce kalaman Sanatocin rashin da'a ne ka Majalisar kuma kana tana iya harzuka al'umma

- Sanatocin da ake zargi sun hada da Sanata Ovie Omo-Agege, Abdullahi Adamu, Abu Ibrahim, Benjamin Uwajumogu, Ali Wakil, Abdullahi Gumel da ma wasu sauran

Akwai yiwuwar wasu Sanatoci 10 za su sha gudumar majalisar dattawa bisa kalaman da suka furta game da canje-canje da majalisar tayi ga jadawalin babban zaben mai zuwa a shekarar 2019.

A sabuwar jadawalin da majalisar ta amince dashi, za'a fara da zaben Sanatoci ne sai na majalisar wakilai ya biyo bayansa, sai kuma zaben gwamnoni da kuma yan majalisar jiha. Zaben shugaban kasa kuma ya zo daga karshe.

Canja jadawalin zabe: Jerin Sanataci 10 da zasu sha gudumar majalisa saboda kalaman adawa

Canja jadawalin zabe: Jerin Sanataci 10 da zasu sha gudumar majalisa saboda kalaman adawa

A yau Talata majalisar ta umurci kwamitin da'a ka da sauraron koken al'umma yayi bincike kan kalamen battanci da aka danganta ga Sanata Ovie Omo-Agege mai wakiltan Delta na tsakiya da wasu Sanatocin guda tara.

DUBA WANNAN: An yankewa wani dalibi mai shekaru 18 da ya sace babur daurin shekara daya

Sauran Sanatocin sune Abdullahi Adamu, Abu Ibrahim, Benjamin Uwajumogu, Ali Wakil, Abdullahi Gumel, Binta Masi Garba, Yahaya Abdullahi, Andrew Uchendu da Umaru Kurfi.

Sanata Dino Melaye (Kogi ta Yamma) ne ya karanta kudirin gudanar da bincike kan Sanatocin da ake zargin su laifin rudar yan Najeriya da cuwa an canja jadawalin zaben ne don a musgunawa Shugaba Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel