Janar ƙeƙe da ƙeƙe: Buhari ya yi watsi da buƙatar ministan shari’a game da dakatar da binciken tsofaffin ministoci Diezani da Bello Adoke

Janar ƙeƙe da ƙeƙe: Buhari ya yi watsi da buƙatar ministan shari’a game da dakatar da binciken tsofaffin ministoci Diezani da Bello Adoke

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, da ta cigaba da bankado duk masu hannu cikin badakalar siyar da rijiyar mai ta Malabu.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito daga cikin wadanda ake zargi akwai tsohuwar ministan albarkatun man fetir, Diezani Allison Maduekwe, tsohon ministan shari’a Bello ADoke, da tsohon ministan mai Dan Atete.

KU KARANTA: Wani direban bankaura ya kira ruwa, ya shiga gaban motar gwamna, ya hana shi tafiya

Wannan umarni na shugaba Buhari ya ci karo da bukatar ministan shari’a Abubakar Malami, wanda ya aika ma Buhari wata zungugeriyar wasika, inda bukaci Buhari ya dakatar da binciken da EFCC ke yi kan badakalar siyar da rijiyan man, mai dauke da gangar mai biliyan 9.

Janar ƙeƙe da ƙeƙe: Buhari ya yi watsi da buƙatar ministan shari’a game da dakatar da binciken tsofaffin ministoci Diezani da Bello Adoke

Buhari da Diezani

A cewar ministan, iya binciken da ya gudanar da ya nuna tsofaffin ministocin basu da hannu cikin badakalar. Sai dai a wani mataki mai cin karo da juna, kwatsa sai Buhari ya aika ma EFCC sabuwar umarni, na cewa kada su fasa, su cigaba da binciken kwakwaf game da lamarin don tabbatar an hukunta duk masu hannu cikin badakalar.

Buhari ya aika wannan umarni ga shugaban EFCC Ibrahim Magu ne a ranar 18 ga watan Janairu, ta hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abb Kyari, a matsayin mayar da martani game da wasikar da Magu ya aike masa yana sanar da shi halin da ake ciki game da binciken.

Cikin takardar da shugaban EFCC, Magu ya aika ma Buhari ya bayyana gano hannun wasu jami’an kamfanin hakar mai ta Royal Dutch Shell da ENI na kasar Italiya cikin badakalar, da kuma hukuncin wata kotu da ta umarci a dawo da wani kaso na kudin da aka siyar da rijiyar man.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel