Dambarwa: Shanu sun shigo a cikin filin jirgi, sun hana jirgi sauka
Gwamnan jihar Ekiti Mista Ayo Fayose ya bayyana takaicin sa game da yadda yace wasu shanu na makiyaya sun ne mi su kawo wa jirgin sa a jihar Ondo cikas yayin da yake so ya sauka a filin sauka da tashi na jirage a garin Akure.
Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a shafin sa na dandalin sada zumunta na Tuwita inda ya bayyana cewa shanun sai da suka hana jirgin sauka na tsawon mintuna 15 kafin daga baya ya samu ya sauka a ranar Lahadin da ta gabata.
KU KARANTA: Kisan Zamfara: Yan sanda sun kama mutane 3
Legit.ng ta samu cewa shgugaban kamfanin jirgin saman na Air Peace mai suna Mista Chris Iwarah ya tabbatar da faruwar hakan inda ya bayyana cewa amma yanzu komai ya wuce.
A wani labarin kuma, Jami'an hukumar tsaron kasar nan ta 'yan sanda dake a filin sauka da tashin jirage na kasa-da-kasa dake a jihar Legas na tunawa da Murtala Muhammad sun tabbatar da kama wani kasurgumin barawo dumu-dumu da laifin sata a cikin jirgi a ranar asabar din da ta gabata.
Haka nan kuma mun samu cewa jirgin da aka kama barawon a cikin sa dai na kamfanin Air Peace ne mai lamba P47139 kuma yana kan hanyar sa ne ta zuwa Abuja daga Legas din.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng