An tsince wata jaririya dauke da takadar wasiya a Birnin Kebbi
- Hukumar Hisbah ta tsince wata jaririya dauke da takadar wasiya a Birnin Kebbi
- An tsince yariyar ne kusa da makarantar ‘Unity College’ da misalin karfe 11 na dare
- Mahaifiyar ta roka a saka wa yariyar suna Aisha don shine sunan mahaifiyarta
Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi a ranar Juma’a, 22 ga watan Disamba ta gabatar da wata jaririya wanda mahaifiyarta ta jefar a Unguwar shiyar Sarakuna kusa da makarantar 'yan mata wato ‘Unity College’ da misalin karfe 11 na dare.
Wannan yariyar dai an tsince ta ne cikin hijab, inda mahaifiyarta ta rubuta wasikar wasiya ta bari tare da ita.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, mahaifiyar jaririn a cikin wasikar ta roka don Allah a kula mata da diyarta, ta ce ta yanke shawarar jefar da ita ne a dalilin matsa lamba da mahaifiyarta ta yi na a kashe jaririyar, wannan yasa ta zabi ta jefar da ita.
Ta ci gaba da cewa tana rokon duk wanda Allah yasa ya tsinci wannan yariyar a saka mata suna Aisha don shine sunan mahaifiyarta, ta kuma yi alkawarin cewa komai dadewa za ta waiwayo 'yarta.
KU KARANTA: Omokri, Fani-Kayode sunyi martini kan hatsarin dan shugaba Buhari
Daraktan Shari'a a hukumar Hisbah a jihar, Alh. Abubakar Muhammad Lanne Augie, ya bayyana cewam wanna shine karo na farko da suka taba ganin irin wannan na a jefar da diya da wasiyya.
Ya yi bayanin cewa rokon da mahaifiyar yarinyar ta yi na a sawa diyarta sunan mahaifiyarta, ya ce sun cika alkawarin, inda suka anso mata 'Court affidavit' dauke da sunan da ta roka a sawa diyar.
Babban daraktan ya kuma yi Allah wadai da yadda yawan jefar da yara kanana ke karuwa a sassan kasar.
A nasa jawabi, shugaban hukumar hisbah ta jihar, Alh. Suleiman Muhammad ya yi kira ga musulmai su kara hada kai don sa ido a ga cewar an kawo karshen wannan lamarin. Ya roki Allah da ya shiryar da wannan matar ya kuma yi addu'a Allah ya raya wanna jariryar.
Idan kuna bukatar karin bayani, zaku iya tuntubi wanna lambar waya: 07064343965.
Allah yasa mu dace.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng