Kiwon lafiya: Jama’a sun guji allurar foliyo a Jihar Yobe
- Yara da dama sun kauracewa allurar rigakafin foliyo
- Wannan abu ya faru ne a Garin Potiskuma na Jihar Yobe
- An yi allurar ne a Fadar Sarkin Potiskuma Ibn Abali
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa an guji allurar rigakafin foliyo a Jihar Yobe da aka yi kwanan nan.

Shugaban wata Kungiya da tayi wa yara allura a Kasar Mister Gitza Chew ya bayyana wannan a Fadar Sarkin Fotiskum, Alhaji Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa, kwanan nan. Gitza yace sama da yara 13,500 su ka guji rigakafin da aka yi.
KU KARANTA: Gwamnatin Jigawa za ta samar da ruwan sha
Labari ya iso mana dai cewa an yi wa yara 77,000 allurar a Kauyukun na Garin Fostiskum kwanakin baya amma wannan karo yara kusan 63,000 kurum aka yi samu saboda rade-radin cewa akwai wasu guba cikin allurar na rigakafin cutar foliyo.
An dai saba samun irin wannan rade-radi game da allurorin rigakafi a kasar wanda ke sa wasu su dauke yaran su daga Makarantu ko inda ake yin allurar. Hakan dai na iya kawo cikas wajen ganin an rabu da cutar ta foliyo a Arewa maso gabashin kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng