Shararren Mawakin Najeriya ya shiga littafin tarihin Duniya
– Mawakin Najeriya Wizkid ya kara samun babban matsayi a Duniya
– Wiz Kid yana cikin littafin tarihin Duniya na wannan shekarar
– Wata waka ce dai da yayi ta jawo masa wannan shararar a bana
Mawakin kasar nan Wiz Kid yana cikin littafin tarihin Duniya na wannan shekarar bayan da ya kece raini da wata waka kwanakin baya.
Mun samu labari cewa fitaccen Mawakin nan na Afrika Ayodeji wanda aka fi sani da Wiz Kid ya kafa tarihi a fadin Duniya inda ya zama Mawakin Afrika na farko da ya taba shiga cikin kundin tarihi na Duniya watau ‘World Guinness record’.
KU KARANTA: Ka ji yadda ake shirin musuluntar da Najeriya
Shararren Mawakin wanda yanzu haka bai da lafiya ya samu wannan matsayi ne bayan wata waka da su kayi tare da fitaccen Mawakin nan na Kasar Canada watau Drake mai suna ‘One Dance’ wanda ta samu shiga cikin wakokin da aka fi ji kaf a Duniya.
Kwanaki can a wajen wani bikin mawaka na Afrika da aka gudanar a Kasar Amurka, an hangi mawaki Wizkid a wani lungu tare da Justin Skye, wata Mawakiyar Amurka wanda wannan ya sa aka dauka soyayya suke yi amma da alamu ba haka abin yake ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Mawakiya Simi ta shigo Gari
Asali: Legit.ng