Dalilai 5 da yasa mata suka fi son ayi musu aiki mai makon su haihu da kansu

Dalilai 5 da yasa mata suka fi son ayi musu aiki mai makon su haihu da kansu

A wani bincike da masana suka kaddamar, sun gano cewa mafi akasarin mata masu juna biyu sun fi shaáwar ayi masu aiki wajen haihuwa a zamanin nan da muke ciki. Sun fi son hakan ne saboda rashin juriwa wajen nakuda a lokacin haihuwa.

Legit.ng ta kawo maku daga cikin dalilan da wasu mata suka ba da;

1. Mafi akasarin mata masu juna biyu na shaáwar ayi masu tiyata ne saboda tsoron zafin nakuda.

2. Wasu kuma dalilin su na son ayi musu aiki shinene gudun kada a masu kara fadin gaban su ta dalilin haihuwa musamman idan jaririn ya kasance kato.

Dalilai 5 da yasa mata suka fi son ayi musu aiki mai makon su haihu da kansu
Dalilai 5 da yasa mata suka fi son ayi musu aiki mai makon su haihu da kansu Hoto: Premium Times Hausa

KU KARANTA KUMA: KUMA! Anyi ruwan bama-bamai a Maiduguri

3. Yin aikin na rage yawan mutuwar jarirai da iyayen su wanda akan samu a lokacin haihuwa sannan da cututtuka kamar su tsinkau-tsinkau da kan kama yara.

4. Wasu likitocin su kan shawarci mata das u bari ayi musu aiki ne don su karbi kudin masu haihuwar ba ayi wa mata aiki ne don su nemi na amincewa da yi wa mata tiyata domin samun kudi.

5. Wasu matan na so ayi musu aiki ne wajen haihuwa don su haihu ranar da suke so. Kamar don ‘ya’yansu su samu ranaku daya da iyayensu.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna son bamu shawara ko bamu labarai tuntube me a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng