Allah zai tona asirin wadanda su ka kashe Sheikh Ja’afar-Shekarau

Allah zai tona asirin wadanda su ka kashe Sheikh Ja’afar-Shekarau

– A shekarar 2007 aka kashe babban Malami Ja’afar Mahmud Adam a Kano

– Lokacin Malam Ibrahim Shekarau ne Gwamnan Jihar Kano

– Ana zargin Gwamnan da hannu cikin kisar Shehin Malamin

Malam Ibrahim Shekarau yace yana addu’a a gano wadanda su ka kashe Malam Jafar.

Tsohon Gwamnan Kano yace har gobe ba zai daina wannan adduar ba.

Sheikh Ja’afar yana cikin manyan Malaman da aka yi a Arewa.

Allah zai tona asirin wadanda su ka kashe Sheikh Ja’afar-Shekarau
Tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau

Yanzu shekaru 10 kenan da kashe Marigayi Sheikh Ja’afar Adam a lokacin da babban Malamin yake tsakiyar limancin sallar asuba a Ranar wata Juma’a a Kano. A wancan lokaci Malam Ibrahim Shekarau ne Gwamna a Jihar.

KU KARANTA: Abubuwa 3 da Osinbajo zai fara da su

Allah zai tona asirin wadanda su ka kashe Sheikh Ja’afar-Shekarau
Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

Kwanaki Jami’an tsaro su ka bayyana cewa sun ga wasu takardu a gidan Sanata Danjuma Goje da ke alakanta kisan Marigayi Ja’afar da kuma Gwamnan Kano na lokacin Ibrahim Shekarau. Malam Shekarau yace dole ‘Yan Sanda su wanke sa.

Ibrahim Shekarau yace ba shi da hannun cikin harkar kisar yana kuma rokon Allah kullum asirin wadanda su ka yi wannan aiki ya tonu bayan da Malaman Jihar kusan 120 su ka ziyarce sa domin ayi addua Inji Jaridar Daily Trust.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dubi abin da wata Budurwa ta ke yi?

Asali: Legit.ng

Online view pixel