Ondo: Sanatan PDP ɗaya tilo a jihar Ondo ya koma APC
Jam’iyyar PDP na cikin tsaka mai wuya musamman a jihar Ondo, yayin da bata kammala shawo kan matsalar cikin gida daya kunno kai ba dangane da waye dantakarar ta, sai ga shi Sanatan ta guda daya tilo ya canza sheka zuwa APC.

[caption id="attachment_1062606" align="alignnone" width="300"] Sen Yele Omogunwa[/caption]
Sanatan PDP dake wakiltar al’ummar Ondo ta kudu a majalisar Dattawa Sanata Yele Omogunwa ya canza sheka zuwa jam’iyyar APC. Wannan yazo ne rana daya kafin gudanar da zaben gwamnan jihar.
Omogunwa ya sanar da haka ne a ranar Alhamis 24 ga watan Nuwamba bayan tuni dama jita jitan ficewar tasa ta cika gari. Sanatan ya tabbatar da ficewar tasa zuwa APC ga kamfanin dillancin labarai a garin Akure.
KU KARANTA: Jegede ne dan takara na PDP a zaben Jihar Ondo
Sanatan wanda ya kasance tsohon kwamishina ne a jihar Ondo karkashin gwamna Mimiko ya koma jam’iyyar APC ne a garin sa Ode-Irele dake karamar hukumar Irele na jihar.
Kamfanin dillancin Labarai ta bayyana cewar ficewar Omonguwa zuwa APC ya nuna cewa dukkanin Sanatoci Uku dake wakiltar al’ummar jihar Ondo a majalisar Dattawa sun koma APC. Idan ba’a manta ba hukumar INEC ta sanya ranar 26 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo.
Za’a iya cewa PDP bata rabu da Bukar ba ta samu Abu.
za ku iya bin kadin labarun mu @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng