Real Madrid Ta Shiga Neman Sayen Dan Wasan Najeriya, Ta Na Shirin Biyan N168bn

Real Madrid Ta Shiga Neman Sayen Dan Wasan Najeriya, Ta Na Shirin Biyan N168bn

  • Rahoto ya nuna cewa Real Madrid na shirin kashe fiye da €100m (N168bn) domin sayen Victor Osimhen daga Galatasaray
  • An ce Osimhen zai ba Kyalian Mbappé damar komawa gefen hagu, yayin da Madrid ke son samun wanda ya kware a zura kwallo
  • Galatasaray ba ta son barin Osimhen ya tafi cikin sauƙi bayan biyan €75m, lamarin da ka iya rikitar da tattaunawar cinikin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Spain - Real Madrid na shirin sayen fitaccen ɗan wasan Super Eagles, Victor Osimhen, daga Galatasaray kan kuɗi sama da euro miliyan ɗari.

Wannan matakin na daga cikin shirin ƙungiyar na sake karfafa gabansu da kuma ba Kylian Mbappé damar komawa matsayinsa na mai buga hagu.

Real Madrid na shirin sayen dan wasan Najeriya, Victor Osimhen
Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen a filin kwallon kafa. Hoto: @sportsdokitor
Source: Getty Images

A cewar rahoton jaridar Punch, Madrid na ganin lokaci ya yi da za ta dawo da cikakken ɗan gaba mai kwarewar zura ƙwallo, gudu da kuma iya buga finareti.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da zarge zarge, yan bindiga sun kutsa coci, sun sace Fasto da matarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osimhen ne ya dace da zabin Real Madrid

Rahoton ya bayyana Osimhen a matsayin dan wasan da ake nema, domina yana da ƙarfi, kuzari, iya zura kwallo a raga tare da tsantsar iya taka leda da suka dace da falsafar gaban Real Madrid.

Kwarewar Victor Osimhen da kuma shahararsa a Galatasaray sun sa Madrid ke kallon ɗaukar sa a matsayin babban abin da ake bukata a kakar gaba.

Hakan zai ba Mbappé ‘yanci a gefen hagu, inda ya fi yin tasiri tun lokacin da yake takawa PSG wasa, yayin da Osimhen zai zama tubalin hari a tsakiyar gaba.

Kalubalen da Real Madrid za ta fuskanta

Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar ba za ta yi sauƙi ba, ganin cewa Galatasaray ta biya euro miliyan 75 don sayen Osimhen daga Napoli.

Kulob ɗin Turkiyyan na muradin dawowa da ribar kuɗin da ya zuba, musamman ganin yadda Osimhen ke taka rawar gani a halin yanzu.

Kara karanta wannan

'Ana cikin tsoro,' 'Yan majalisar sun yi zazzafar muhawara kan rashin tsaro

Rahoton jaridar The Nation ya kuma nuna cewa idan sauran manyan ƙungiyoyin kwallo suka shiga zawarcin Osimhen, farashin zai iya wuce euro miliyan 100 cikin sauƙi.

A gefe guda, rashin tabbas kan makomar Vinicius Junior a Madrid na iya sauƙaƙa cinikin Osimhen.

Rahoto ya nuna cewa Real Madrid na burin sayen Osimhen don kara karfin gabanta.
Dan wasan Super Eagles, Victor Osimhen a filin wasan kwallon kafa. Hoto: @victorosimhen9
Source: Getty Images

Tasirin Osimhen idan ya shiga Real Madrid

Rahotanni sun ce Vini ya sanar da kulob ɗin cewa ba zai sabunta kwantiraginsa ba sai an yi wasu sauye-sauye, musamman bayan rashin jituwa tsakaninsa da Xabi Alonso.

Idan Vinicius Junior ya tafi ko kuma ya rasa gurbi a gefe, hakan zai ba Mbappé damar komawa gefen hagu gaba ɗaya, sannan Osimhen ya mamaye tsakiyar gaba.

Rahoto ya bayyana cewa zuwan Osimhen kungiyar Madrid zai iya girgiza LaLiga baki ɗaya tare da kawo sauye-sauye a kasuwar cinikin Turai.

Idan an kulla wannan ciniki, zai iya zama ɗaya daga cikin mafi tsada a bazarar 2026, kuma Real Madrid na kallon shi a matsayin jarumin da zai kawo sakamako nan take.

Martanin Furyam da Namunaye kan sayen Osimhen

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu masu sharhi kan wasannin kwallon kafa daga gidan rediyon Globe FM Bauchi, Saminu Adamu Namunaye da Bashir Khalid Furyam.

Kara karanta wannan

'Dan adawar Kamaru, Bakary ya tsallake tarkon Paul Biya, ya gudu kasar Gambiya

Saminu Adamu Namunaye ya bayyana cewa:

"Rahoton da ke cewa Real Madrid na son sayan Victor Osimhen kan Yuro miliyan 100 abu ne mai ban sha'awa matuka. Wannan yarjejeniya tana nuna irin girma da muhimmancin ɗan wasan Najeriyar a idon manyan ƙungiyoyin Turai.
"Idan har hakan ta tabbata, Osimhen zai zama babban jari ga Madrid. Gudunsa da ƙarfinsa na iya dacewa da tsarin gaban Real Madrid. Sai dai, farashin Yuro miliyan 100 ba ƙaramin abu ba ne, Real na buƙatar yin lissafi sosai kafin yanke hukunci.
"Babban kalubalen shine ko Real Madrid za ta iya biyan kuɗin da Galatasaray ke bukata kafin kowa. Ko yaya za ta kaya dai, Najeriya na alfahari da ɗan wasanta Osimhen."

Shi kuma Bashir Khalid Furyam ya ce:

"Gaskiyar magana, Victor Osimhen ya cancanci duk wani kuɗi da za a iya biya domin sayan shi daga Galatasaray. Shi ne ɗaya daga cikin 'yan wasan gaba mafi kyau a duniya a wannan lokacin.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

"Duk da haka, Real Madrid ta san cewa yanzu kasuwa tana da tsada saboda ƙarancin 'yan wasan gaba. Ya kamata su hanzarta domin akwai wasu ƙungiyoyi da suke nuna sha'awar ɗan wasan Najeriyar a Turai."

Man United na da burin sayen Osimhen

Tun da fari, mun rahoto cewa, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ci burin sayen Victor Osimhen tun lokacin da ya na Napoli.

A wancan lokaci, Man United ta shiga tattaunawa da Napoli don sayen Osimhen, wanda aka sanya farashinsa a Yuro miliyan 75.

Victor Osimhen ya dan kwashe watanni yana taka leda a kungiyar Galatasaray a matsayin dan wasan aro, kafin kungiyar ta saye shi daga Napoli.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com