Messi da 'Yan Wasan Kwallon Kafa 4 da Suka Fi Yawan Lashe Kyautar Ballon d'Or
Ballon d'Or, wacce hukumar kwallon kafar Faransa ta kafa a 1956, ita ce kyauta mafi girma da ake ba dan kwallon kafa, wacce ke nuna makurar kwarewar dan wasa.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A tsawon tarihin ba da wannan kyauta, akwai fitattun 'yan wasa biyar da suka lashe ta sau uku ko fiye da haka, alamar da ke nuna kwarewarsu a taka leda.

Source: Getty Images
Wannan rahoto, ya yi nazari kan 'yan wasan da suka fi yawan kyautar Ballon d'Or, tun daga kafa ta, har zuwa ranar 22 ga Satumba, 2025 da aka samu sabon gwarzo, inji rahoton ESPN.
'Yan kwallo 5 da suka fi lashe Ballon d'Or
An gudanar da taron ba da kyautar Ballon d'Or ta 2025 ne a Paris, inda fitaccen dan wasa, Ousmane Dembele ya samu kyautar a karon farko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin 'yan kwallon da suka fi kowa yawan lashe kyautar Ballon d'Or:
1. Lionel Messi

Source: Getty Images
Lionel Messi shi ne ja-gaba a jerin 'yan kwallon kafa da suka lashe kyautar Ballon d'Or, inda ya lashe kyautar har sai tawas.
Messi ya lashe Ballon d'Or a shekarun: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021, da kuma 2023.
Ba sai an fada ba, tuni duniya ta shaida cewa Messi, dan asalin Argentina, ya kasance dan wasa mai hazaka, iya taka leda da kuma zura kwallaye.
Messi ya lashe mafi yawan kyautar Ballon d'Or a lokacin da yake buga wasa a Barcelona, inda kwarewarsa a buga tamaula ya sa kungiyar ta lashe kofin zakarun turai a lokuta daban daban.
A shekarar 2021 ne Messi ya lashe Ballon d'Or, lokacin yana buga wasa a Paris Saint-Germain (PSG), sai kuma 2023 da ya lashe kyautar bayan Argentina ta lashe kofin duniya.
2. Cristiano Ronaldo

Source: Getty Images
Cristiano Ronaldo ne ke biya da Messi, bayan da ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau biyar, watau a shekarun 2008, 2013, 2014, 2016, da 2017.
Dan wasan na Portugal, ya kasance kwararre a fagen taka leda, kuma yadda ya yi fice a zura kwallaye a ragar abokan hamayya, ya sanya shi ya zamo babban dan wasa.
Ronaldo ya fi lashe kyautar Ballon d'Or a lokutan da yake taka leda a Manchester United da kuma Real Madrid, inda ya lashe kyautar a 2016 da 2017 saboda nasarar da ya samu a gasar zakarun Turai.
Duk da yana da shekaru 40, yadda Ronaldo yake ci gaba da buga wasa a gasar Saudi Pro League ya nuna ƙwazonsa, amma dai har yanzu akwai tazara tsakaninsa da Messi a daukar Ballon d'Or.
'Yan kwallo 3 masu Ballon d'Or 3
Kafin Messi da Ronaldo, rahoton UEFA ya nuna cewa 'yan wasa 3 ne kawai suka taba lashe kyautar Ballon d'Or da ta kai sau uku:
- 3. Johan Cruyff (1971, 1973, 1974)
- 4. Michel Platini (1983, 1984, 1985)
- 5. Marco van Basten (1988, 1989, 1992)
Tsarin da Cruyff ya kawo na wasan “Total Football” sun sauya kwallon kafa, yayin da basirar Platini a tsakiyar fili ta ƙara wa Juventus ƙarfi.
Kwazon Van Basten na zura ƙwallaye ne ya sanya ya yi fice a zamaninsa, duk da cewa yawan raunuka ya kawo ƙarshen buga kwallonsa da wuri.
A 'yan shekarun nan, an samu bullar sababbin jini a harkar buga kwallo. Kamar Kyalian Mbappe, wanda ya lashe Ballon d'Or a 2024 a karon farko, bayan nuna bajinta a PSG da Faransa.
Ousmane Dembélé ya lashe Ballon d'Or
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Ousmane Dembélé, ya lashe kyautar Ballon d'Or a karon farko, bayan kwarewarsa da ta taimakawa PSG ta lashe kofin zakarun Turai.
Dembélé ya lashe wannan kyauta ta Ballon d'Or, a matsayin zakaran dan wasan kwallon kafa da ya fi kowane kokari a maza a kakar wasan da ta gabata.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Bam ya tarwatse da yara 'yan firamare suna wasa cikin aji a Benue
'Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta PSG ya samu wannan nasara ne bayan doke matashin dan wasan Barcelona, watau Lamine Yamal.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


