Duk da Uwarsa Musulma ce, Paul Pogba Ya Fadi Silar Karbar Addinin Musuluncinsa

Duk da Uwarsa Musulma ce, Paul Pogba Ya Fadi Silar Karbar Addinin Musuluncinsa

  • Paul Pogba wanda ya bugawa Manchester United ya na cikin musulman ‘yan wasan kwallon kafa a duniya
  • Mahaifiyar ‘dan wasan, Yeo Pogba musulma ce amma kuma ba ita ta yi sanadiyyar karbar musuluncinsa ba
  • Mafi yawan abokan Paul Pogba musulmai ne, ganin yadda suke ibada ya sa ya bar addinin da yake kai a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

France - Paul Pogba yana cikin taurarin ‘yan wasan kwallon kafa da ke kan addinin musulunci, hakan ya sa ya yi fice a duniya.

Mahaifiyar Paul Pogba musulma ce, amma ba ta matsawa shi ‘dan kwallon ko sauran ‘yanuwansa uku su yi koyi da addininta ba.

Paul Pogba
Paul Pogba ya canza addini zuwa musulunci Hoto: Bee Sports
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da The Life Times, tsohon ‘dan kwallon na Manchester United ya taba ba da labarin yadda ya zama musulmi.

Kara karanta wannan

Jill Stein da ‘yan takaran da suka nemi mulkin Amurka tare da Trump da Harris

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani Abba Katiti ya dawo da wannan hira da ya wallafa ta a dandalin X kwanaki.

Paul Pogba yake cewa zahirin musulunci ya sha bam-bam da irin labaran da ake ji a duniya. An saba alakanta addinin da ta’addanci.

“Musulunci ba shi ne abin da kowa yake gani ba, ta’addanci. Abin da mu ke gani a gidajen labarai dabam. Abu ne mai kyau.”
“Ya sa na canza, na fahimci abubuwa a rayuwa. Ina tunani, watakila ya sa na kara samun aminci a rai na.
“Ba a musulmi aka haife ni musulmi ba, ko da mahaifiyata musulma ce. Haka nan na girma, ina girmama kowa.

- Paul Pogba

Abokai sun jawo hankalin Paul Pogba

A rahoton Independent, ‘dan kwallon ya ce ya na da abokai musulmai, a dalilin haka ya karbi addinin saboda yawan tattaunawa da su.

Kara karanta wannan

Sheikh Dutsen Tanshi: Darasin da Tinubu zai koya daga nasarar Donald Trump a Amurka

Daga jefawa abokan tambayoyi, sai ya fara yin bincike game da adinin, kafin a ce mene kuwa sai ga shi ya fara bin su zuwa sallah.

A yau sai ‘dan wasan tsakiyan na kungiyar Juventus a Italiya ya na yin salloli biyar kuma ya na zuwa aikin hajji a kasar Saudi mai tsarki.

An hana Pogba buga kwallon kafa

Kwanaki aka ji cewa an samu Paul Pogba da laifin amfani da kwayoyin karin kuzari don haka aka haramta masa buga kwallo a duniya.

Ba Pogba ne dan wasa na farko da aka kama da wannan laifi ba. Diego Maradona da Andre Onana su ma sun taba fuskantar fushin FIFA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng