Paul Pogba ya yi ritaya daga Faransa a kan zargin Musulunci da ta’addanci

Paul Pogba ya yi ritaya daga Faransa a kan zargin Musulunci da ta’addanci

- Ana rade-radin Paul Pogba ba zai kara bugawa kasarsa Faransa kwallo ba

- Hakan na zuwa ne bayan kalaman da shugaban Faransa ya yi a kan Islama

- ‘Dan wasan mai shekara 27 ya buga wasanni 72, ya kuma lashe kofin Duniya

Rade-radi daga jaridun kasashen waje su na nuna ‘dan wasan kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya ajiye bugawa kasarsa ta Faransa kwallo.

Paul Pogba mai buga tsakiya ya dauki wannan mataki ne bayan da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya caccaki addinin Musulunci.

Emmanuel Macron ya zargi addinin musulunci da zama silar ta’addanci a kasashen Duniya.

KU KARANTA: Tauraron Super Eagles Ahmed Musa ya bar kungiyar Saudiya

Bayan kalaman shugaban kasar na Faransa a ranar Juma’a, gwamnatin Faransa ta kuma karrama wani malami da ya yi batanci ga Annabi.

Rahotanni daga jaridu da-dama daga gabas ta tsakiya sun bayyana cewa ‘dan wasan mai shekara 27 a Duniya ya ajiye bugawa kasar Faransar kwallo.

Kawo yanzu tsohon ‘dan wasan na Juventus bai tabbatar da wannan rade-radi ba, haka zalika da shi da kungiyar kwallon Faransa ba su musanya hakan ba.

Tauraro Paul Pogba musulmi ne wanda kuma ba ya boye addininsa. ‘Dan wasan Duniyan ya halarci Hajji da Umrah a kasar Saudi Arabia sau da dama.

KU KARANTA: Suarez ya bada labarin abin da ya faru da shi a Barcelona

Paul Pogba ya yi ritaya daga Faransa a kan zargin Musulunci da ta’addanci
Pogba ya ci wa kasar Faransa 10 Hoto: www.thesun.co.uk
Asali: UGC

‘Dan wasan da ya lashe kofin Duniya a 2018 ya na ganin karrama malamin nan da aka yi da kuma kalaman shugaba Macron cin kashi ne ga addininsa.

Bayan kirista, babu wadanda su ke da mabiya irin musulmai a kasar Faransa, inda Pogba ya fito.

Kwanaki kun ji cewa Manchester United ta saye sababbin ‘yan wasan kwallo. Kungiyar ta kashe kudi ana makudan kudi ana daf da rufe cinikin 'yan wasa.

Edinson Cavani, Alex Telles, Facundo Pellistri, da Amad Diallo sun koma Manchester United.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng