Kwana 1 da Lashe Gasar Champions League, Madrid Ta Sayi Mbappe Daga PSG

Kwana 1 da Lashe Gasar Champions League, Madrid Ta Sayi Mbappe Daga PSG

  • Shahararren dan wasan Faransa, Kylian Mbappe ya koma kungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid bayan sanya hannu a kwantiragi
  • Mbappe ya sanya hannu a takardun kwantiragi inda ake sa ran Madrid za ta sanar da shi a matsayin sabon ɗan wasanta a makon gobe
  • Legit Hausa ta tattauna da wasu magoya bayan Madrid da Barcelona kan wanna yarjejejeniya na Mbappe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Paris - Dan wasan gaban Faransa, Kylian Mbappe ya sanya hannu a kwantiragi da kungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid.

Dan wasan mai shekaru 25 ya jona Madrid ne kwana ɗaya bayan sun lashe gasar zakarun Turai ta Champions League.

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan kisan sojoji a Abia, ya fadi matakin dauka

Kylian Mbappe ya sanya hannu a kwantiragi domin komawa Madrid
Dan wasan Faransa, Kylian Mbappe ya koma Real Madrid daga PSG. Hoto: Alex Grimm.
Asali: Getty Images

Mbappe ya sanya hannu a dukkan takardu

Dan jarida daga kasar Italiya, Fabrizio Romano shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Lahadi 2 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Romano ya ce an kammala dukkan wasu ka'idoji kan kwantiragin inda Mbappe ya sanya hannu.

"Kylian Mbappe zuwa Real Madrid ta tabbata, duk wata takarda ta kwantiragi an tabbatar da ita kuma an sanya hannu."
"Real Madrid za ta sanar da siyan Mbappe a matsayin sabon ɗan wasanta a makon gobe bayan lashe gasar Champions League."
"Mbappe ya yanke shawarar barin PSG a watan Faburairu, yanzu za a iya cewa ya dawo sabon ɗan wasan Real Madrid."

Tattaunawar Legit Hausa da wasu kan Mbappe

Legit Hausa ta tattauna da wasu magoya bayan Madrid da Barcelona kan wanna yarjejejeniya na Mbappe

Shamsudden Sani ya ce wannan abin farin ciki ne ga Madrid saboda daman sun dade suna dakon Mbappe.

Kara karanta wannan

Ronaldo ya fashe da kuka yayin da Al Nassr ta yi rashin nasara a gasar cin 'kofin sarki'

"Abin farin ciki ne samun Mbappe inda hakan za kara inganta karfin kungiyar da kuma gasa."
"Babu wani batun sake Rodrigo ko wani dan wasa domin Mbappe ya zo kowa kawai ya iya allonsa ya wanke."

- Shamsudden Sani

Matashin ya kuma kore hasashen cewa Mbappe zai iya lalacewa kamar Hazard inda ya ce shekarunsu ma ba daya ba ne a lokacin.

Wasu ƴan Barcelona sun kushe lamarin inda suka yi fatan Mbappe ya kasance kamar Hazard idan ya zo Madrid.

Abdul Barca ya ce:

"Tabbas Mbappe dan wasa ne mai kyau amma ba dole ya taka rawa ba, muna fatan ya dawo kamar Hazard lokacin da ya zo Madrid."

Umar Boka ya ce shirme ne Mbappe ko a PSG ma bai tsinana komai ba haka zai zo a banza.

Kylian Mbappe ya tabbatar da barin PSG

A wani labarin, kun ji cewa Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa, Kylian Mbappe ya sanar da barin ƙungiyar Paris Saint-Germain watau PSG a karshen kakar wasa ta bana.

Mbappe ya bayyana cewa zamansa ya zo ƙarshe a PSG a wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ranar Jumu'a 10 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.