Zaratan Mata Musulmi 5 da Ake Fafatawa da su a Wasannin Kwallon Kafa

Zaratan Mata Musulmi 5 da Ake Fafatawa da su a Wasannin Kwallon Kafa

Tun bayan da mata su ka fara murza leda a hukumance a ranar 7 ga watan Mayu, 1881 a filin wasan Hibernian da ke Edinburgh ake ta samun mata suna nuna bajinta a fagen.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

A wannan rahoton na Legit Hausa, mun zakulo muku mata musulmai biyar da tauraruwarsu ke haskawa a fagen kwallon kafa.

Mata 'yan wasa
Wasu zaratan mata 'yan wasan kwallon kafa a duniya Hoto: Nouhaila Benzina, Asisat Oshoala , Khadija Shaw
Asali: Facebook

Mata musulmi a fagen wasanni

1. Asisat Lamina Oshoala

Zakakurar 'yar kwallo ce da ta shahara a duniya. Yar Najeriya ce, bayerabiya haifaffiyar Ikorodun jihar Lagos. An haife ta a shekarar 1994, 9 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Sabani ya barke tsakanin 'yan awaren Biafra da ke fafutukar a tsaga Najeriya gida 2

Ta zama mace da ta fi kowa zura kwallaye a wasan yan kasa da shekaru 20 na FIFA a shekarar 2014.

Haka kuma ta nuna bajinta a wasan African Women Championship shi ma a shekarar 2014 inda ta zama ta biyu a mafi zura kwallaye a gasar.

Asisat Oshoala ta bugawa kungiyoyi irin su ta Najeriya, da Rivers Angels, da Liverpool FC, Arsenal, da Dalian Quanjian F.C. sai kuma FC Barcelona Femení.

2. Khadija Monifa "Bunny" Shaw

Fitacciyar 'yar wasan kwallon kafar Manchester City ce 'yar asalin Jamaica.

'Yar wasar da ta samu sunan Bunny saboda tsagwaron kaunar dake tsakaninta da karas, ita ce ke rike da kambun 'yar wasan da ta fi kowa zura kwallaye a Jamaica tsakanin maza da mata.

An haife ga a ranar 31 Janairu, 1997. Kuma ta murza leda a kungiyar kwallon kafa ta gida wato Girondins de Bordeaux.

Ta bugawa kungiyoyi da dama wasa ciki har da Tennessee Lady Volunteers soccer da Jamaica women's national association football.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun kai hare-hare kan 'yan ta'addan Arewa da barayin mai a Niger-Delta

Khadija ta rike kambun 'yar wasan kwallon kafa ta Guardian a shekarar 2018 wanda sai 'yar wasa ta buga bajinta za ta same shi.

3. Nouhailla Benzina

An haife ta a Kenitra da ke Morocco a ranar 11 Mayu 1998. Nouhailla ta dauki hankalin duniya da shigar da ta ke wajen buga wasanni, cikin rufe jikinta baki daya. Ta zama mace ta farko da ta yi haka a shekarar 2003 a gasar cin kofin duniya FIFA.

Lamarin da kasashe irinsu Faransa ke ta suka a wancan lokaci, ita kuwa ko a jikinta domin a haka ta ci gaba da murza leda.

Yanzu haka ita ce mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafar mata ta Morocco.

4. Hanane Ait El-Haj

Shahararriyar 'yar wasan kwallon kafa ce, kamar Nouhailla, ita ka 'yar asalin Morocco ce.

An haife ta a shekarar 1994, a ranar 2 ga watan Nuwamba.

Ta buga wasanni a kungiyoyi da dama ciki har da kungiyar kwallon kafar mata ta Morocco,da AS Far women, da Zaragoza club de Futbol Fenenino.

Kara karanta wannan

Lebanon: Hizbullah ta kai harin ramuwar gayya kan kasar Isra'ila

A shekarar 2022, kungiyarta ta yi nasara a wasan zakarun mata ta CAF, ta kuma lashe gasar tare da AS FAR sau shida.

5. Hawa Cissoko

Daya daga zakakuran musulman mata dake taka leda a duniya, an haifi Hawa Cissoko a Paris ranar 10 ga watan Afrilun 1997.

Ta fara murza leda ne a shekarar 2014. Hawa Cissoko ta fara wasan da kungiyar FC Solitaire daga baya kuma kungiyar Paris Saint German ta mika mata goron gayyata a tana da shekaru 12.

Tauraruwar matashiyar ta fara walwali ne a shekarar 2014-15 a kungiyar ta Saint German, daga bisani ta wulwula kungiyar Olympique de Marseille a 2017.

An haramta mata buga wasanni biyar bayan ta samu kacaniya da wata 'yar wasan kwallon kafar Aston Villa. Duk da Hawa na sanya hijabi, ta kan cire shi idan ta zo buga wasanni.

Wasanni: Super Falcons ta lallasa Bafana-Bafana

Kara karanta wannan

Yadda ake rijista: Rundunar sojin Najeriya ta sanar da daukar sabbin sojoji a 2024

Kun samu labarin cewa kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya, Super Falcons ta yi dauki kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika.

Kungiyar ta samu wannan nasara ne bayan ta lallasa Afrika ta kudu da ci hudu a gasar da ya gudana a shekarar 2018.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.