Kungiyar PSG tana kokarin dauko Ronaldo, ya buga kwallo tare da Messi, Neymar, da Ramos

Kungiyar PSG tana kokarin dauko Ronaldo, ya buga kwallo tare da Messi, Neymar, da Ramos

  • ‘Dan wasa Kylian Mbappé ya dage sai ya bar kungiyar Paris Saint-Germain
  • Rahotanni sun ce Kylian Mbappé yana so ya koma buga wasa a Real Madrid
  • PSG za ta dauko Cristiano Ronaldo daga Juvenuts idan har ta rasa Mbappé

Kylian Mbappé zai cigaba da wasa a Faris?

Spain - Rahotanni daga kasar Sifen suna nuna cewa Kylian Mbappé ya na kokarin barin kungiyar PSG da nufin ya koma buga wa Real Madrid kwallo.

Idan tashin ‘dan wasan kasar Faransa, Kylian Mbappé ta tabbata zuwa Real Madrid, kungiyar za ta maye gurbinsa ne da gwarzonsa, Cristiano Ronaldo.

Majiyoyi irinsu Pedrerol, Cadena SER da El Transistor duk sun kawo rahoto cewa a yau Mbappé mai shekara 22 zai bukaci ya bar Paris Saint-Germain.

AS ta ce Matashin ‘dan wasan gaban zai zauna da shugaban kungiyar PSG, Nasir Al-Khelaifi a ranar Talata domin bijiro da maganar barin kulob din.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Ana rade-radin Mbappé ya ki halartar bikin da abokin aikinsa, Marco Verratti ya shirya domin murnar zagagowar ranar haihuwarsa a daren da ya wuce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da Paris Saint-Germain ta dauko Lionel Messi daga kungiyar Barcelona, Kylian Mbappé bai da niyyar sabunta kwantiraginsa da kungiyar ta Faransa.

Ronaldo tare da Messi
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo Hoto: football-italia.net
Asali: UGC

Bisa dukkan alamu, tauraron ‘dan kwallon ya dauki hudubar masu ba shi shawara ya je babban kulob domin tauraruwarsa ta haska da kyau a Duniya.

Wa’adin ‘dan wasan gaban zai kare ne a tsakiyar 2022, shiyasa PSG za ta saida shi ga Real Madrid idan har ya hakikace, gudun ka da ta rasa shi a banza.

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da riga daya?

Muddin PSG ta saida Mbappé zuwa ga Real Madrid, za ta yi amfani da kudin da ta samu ne wajen sayen babban ‘dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta ce a karbe N241m da aka karkakatar daga ofishin Hadimin Shugaba Buhari

Shi ma Ronaldo ya na shekarar karshe a Juventus, kuma kungiyar a shirye ta ke ta saida shi a kakar cefanen bana domin gudun ta tashi a tutar babu a 2022.

Wannan zai bada dama Nasir Al-Khelaifi ya hada Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a wuri daya.

Masu sha'awar kwallon kafa za su so ganin taurari; Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, Neymar Jr., Sergio Ramos, wanda da abokan gaba ne, a kulob daya.

Messi ya bar Barcelona

A makon da ya wuce ne babban ‘dan wasan Duniyan nan, Lionel Messi ya tashi daga Barcelona, ya koma buga kwallo a kungiyar PSG da ke kasar Faransa.

Tsohon kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos ya yi wa Lionel Messi kyakkyawar tarba, ya yi masa tayin su zauna tare a gidansa kafin ya samu matsuguni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel