Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta mata (Super Falcons) ta yi nasarar lashe gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika.
Kungiyar ta samu wannan nasara ne a yau, Asabar, bayan fafatawa a wasan karshe da kasar Afrika ta kudu.
Kungiyar Super Falcons ta samu nasarar zura kwallo 4 a ragar kasar kungiyar Bafana Bafana ta Afrika ta Kudu.
An tashi wasan Najeriya na da kwallo 4 a raga yayin da kasar Afrika ta Kudu ke da kwallo 3 a raga bayan wasan ya shiga karin lokaci.

Yanzu Yanzu: Tawagar mata na kungiyar kwallon kafan Najeriya su yi nasarar lashe wasan matan Afrika
Source: Twitter
Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murna ga kungiyar super falcons.
KU KARANTA KUMA: Dan takarar shugaban kasa ya koma APC, ya goyawa Buhari baya
Kazalika, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya taya kungiyar Super Falcons murna.
Wannnan shine karo na 9 da kungiyar super falcons ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng