Nigeria Vs Ghana: An Fitar da Jerin Ƴan Wasa 4 da Ba Za Su Buga Wasa a Yau Ba

Nigeria Vs Ghana: An Fitar da Jerin Ƴan Wasa 4 da Ba Za Su Buga Wasa a Yau Ba

  • Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da takwarorinta na Ghana da Mali a cikin wannan wata na Maris
  • Ana sa ran wasannin da aka shirya gudanarwa a Morocco, za su kayatar da mutane tun bayan fafatawar da tawagogin suka yi a gasar AFCON ta 2023
  • Sai dai kuma, an samu bayanai cewa akwai wasu ƴan ƙwallo 4 da ba za su bugawa Najeriya wasan ba, ciki kuwa har da Victor Osimhen

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta koma filin wasa a karon farko tun bayan da aka kammala gasar AFCON, a ƙasar Ivory Coast.

Kara karanta wannan

An haramta wa ƴan ƙwallo Musulmi yin azumi a Faransa, wani ɗan wasa ya ɗauki mataki

Jerin 'yan wasa 4 da ba za su buga wasan Najeriya da Ghana ba
Nigeria Vs Ghana: Yan wasa 4, ciki har da Osimhen ba za su buga wasan yau ba
Asali: Twitter

A halin yanzu babu wani tsayayyen mai horas da ƴan wasan Super Eagles, sai dai an ga ƴan wasan na zumuɗin fafatawa da ƙasar Ghana da Mali.

Najeriya za ta buga wasan sada zumunta

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa Super Eagles za ta kara da Ghana a yau Juma'a, 22 ga watan Maris, sannan ta fafata da Mali a ranar 26 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa za a buga wasannin ne a matsayin 'sada zumunta' gabanin fara wasannin shiga gasar cin kofin duniya na FIFA 2026.

Yayin da aka ware ƴan wasa 26 da za su buga wa Super Eagles ƙwallo, an gano cewa akwai ƴan wasa hudu da suka samu matsalar rauni.

Ga jerin ƴan wasan a ƙasa:

Victor Osimhen

Fitaccen ɗan wasan Najeriya na gaba, ya gamu da rauni a kungiyar ƙwallonsa ta Napoli bayan dawowa daga gasar AFCON.

Kara karanta wannan

Sarki Charles III ya yi bankwana da duniya? Gaskiya ta bayyana

Kocin Napoli, Frances Calzona, ya ce Osimhen na jinyar jikinsa har yanzu. Sannan a gida Najeriya ma, an ruwaito cewa ba zai buga wasansu da Ghana ba.

Tyronne Ebuehi

Duk da cewa bai samu damar buga wasa a gasar AFCON 2023 ba, Tyronne Ebuehi ya shiga jerin ƴan wasan Super Eagles yana da shekaru 28. Sai dai shi ma ba zai buga wasansu da Ghana ba.

Super Eagles ce ta sanar da hakan, inda ta ce ɗan wasan na baya na fama da raunuka ƙafa kuma ba zai iya buga wasa a wannan kakar ba.

Taiwo Awoniyi

Shi ma dai Taiwo Awoniyi, dan wasan gaba ba zai buga wa Super Eagles wasa ba duk da ya yi tashe a gasar AFCON 2023.

Ba a jima ba Awoniyi ya warke daga wani rauni da ya shafe watanni uku yana jinya, yanzu kuma ya sake samun wani raunin.

Gabriel Osho

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojojin Najeriya sun halaka wani shugaban ƴan bindiga da mayakansa

Ɗan wasan gaba na Najeriya da na Luton Town, Gabriel Osho ba zai buga wasannin sada zumunta tsakanin Najeriya da Ghana, Mali ba.

Osho ya samu rauni ne a lokacin da tawagarsa ta kara da Crystal Palace a gasar Premier League.

Duba jerin sunayen a nan ƙasa, kamar yadda @PoojaMedia ya wallafa a shafinsa na X:

Kocin Najeriya Peseiro ya ajiye aiki

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa kocin Najeriya Jose Peseiro, ya yi murabus daga mukamin mai horas da tawagar Super Eagles.

Murabus dinsa ya biyo bayan karewar wa'adin kwantiraginsa na horar da yan wasan, inda rahotanni suka bayyana cewa ya ki amincewa da sabon tsarin albashinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel