Zakarun Turai: Yadda Jadawalin Kwata Final Na UEFA Champions League Ya Kasance
- Bayan kammala wasannin 'yan 16 a gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA Champions League, yanzu kuma an iso matakin kwata final
- Hukumar gudanarwar gasar ta UEFA, a wannan Juma'ar, ta fitar da jadawalin wasannin da za a buga a zagayen kwata final din
- Za a fara buga zagayen farko na kwata final a gasar cin kofin zakarun Turai na 2023/24 a ranar 9 da 10 ga watan Afrilu, 2024
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA Champions League ta iso matakin kwata final, inda ya rage saura tawaga takwas da za ta fafata a wannan mataki.
Hukumar gudanarwar gasar ta UEFA, a wannan Juma'ar, ta fitar da jadawalin wasannin da za a buga a kwata final.
Manchester City ta Pep Guardiola za ta iya zama kungiya ta biyu kacal da ta lashe kofin gasar zakarun Turai a jere
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo UEFA.com, Za a buga zagayen farko a ranar 9 da 10 ga watan Afrilu, 2024, yayin da za a buga zagaye na biyu a ranar 16 da 17 ga Afrilu, 2024.
Ga yadda jadawalin ya ke:
UEFA Champions League 2023/2023 - Kwata final
Arsenal | Vs | Bayern Munich |
Atletico Madrid | Vs | Borussia Dortmund |
Real Madrid | Vs | Manchester City |
Paris Saint-Germain | Vs | Barcelona |
UEFA: Yaushe za a buga kwata final?
Shafin wasanni na Sporting News ya wallafa cewa za a fara buga zagayen farko na kwata final a gasar cin kofin zakarun Turai na 2023/24 a ranar 9 da 10 ga watan Afrilu, 2024.
Za a gudanar da wasannin zagaye na biyu na kwata final din bayan mako guda da kammala zagayen farko a ranar 16 da 17 ga watan Afrilu.
Jadawalin wasannin kusa da na karshe
Bayan kammala wasannin kwata final, ga kuma yadda ake hasashen kungiyoyin kwallon kafar za su kara da juna a wasan kusa da na karshe na gasar ta UEFA.
Atletico Madrid/Borussia Dortmund | Vs | Paris Saint-Germain/Barcelona |
Arsenal/Bayern Munich | Vs | Real Madrid/Manchester City |
UEFA: Yaushe za a buga wasannin gaba?
Za a buga zagayen farko na wasan kusa da na karshe a gasar UEFA 2023/24 a ranar 30 ga watan Afrilu da 1 ga watan Mayu, 2024.
Haka kuma za a buga zagaye na biyu na wasan kusa da na karshe bayan mako guda da kammala zagayen farko a ranar 7 da 8 ga watan Mayu.
UEFA: Cikakken jadawalin wasanni
Ga cikakken jadawalin wasannin da ya hada da; tawagannin da za su kara da juna da kuma ranar buga wasannin.
Wasannin kwata final
Haduwar tawaga | Ranakun zagayen farko | Ranakun zagaye na biyu |
Arsenal vs. Bayern Munich | 9/10, Afrilu, 2024 | 16/17, Afrilu, 2024 |
Atletico Madrid vs. Borussia Dortmund | 9/10, Afrilu, 2024 | 16/17, Afrilu, 2024 |
Real Madrid vs. Manchester City | 9/10, Afrilu, 2024 | 16/17, Afrilu, 2024 |
Paris Saint-Germain vs. Barcelona | 9/10, Afrilu, 2024 | 16/17, Afrilu, 2024 |
Wasannin kusa da na karshe
A wannan bayanin na kasa, za mu yi amfani da KF a matsayin 'kwata final', sannan TN a matsayin 'tawagar da ta yi nasara.
Haduwar tawaga | Ranakun zagayen farko | Ranakun zagaye na biyu |
TN a wasan KF 2 Vs TN a wasan KF 4 | 30 ga Afrilu/1 ga Mayu | 7/8, Mayu, 2024 |
TN a wasan KF 1 Vs TN a wasan KF 3 | 30 ga Afrilu/1 ga Mayu | 7/8, Mayu, 2024 |
Wasan karshe
A wannan bayanin na kasa, za mu yi amfani da WKK a matsayin 'wasan kusa da na karshe', sannan TN a matsayin 'tawagar da ta yi nasara.
Haduwar tawaga | Ranar buga wasa | Lokacin buga wasa |
TN a wasan WKK 1 Vs TN a wasan WKK 2 | 1 ga Yuni, 2024 | Karfe 1:00 na rana |
Jerin kungiyoyin da aka fitar
Ga cikakken jerin kungiyoyin da aka fitar da su daga gasar zakarun Turai ta 2023/24.
- Red Star Belgrade (SER)
- Young Boys (SWI)
- Royal Antwerp (BEL)
- Union Berlin (GER)
- Braga (POR)
- Benfica (POR)
- RB Salzburg (AUS)
- Feyenoord (NED)
- Celtic (SCO)
- Lens (FRA)
- Sevilla (SPA)
- Galatasaray (TUR)
- Man United (ENG)
- Shakhtar Donetsk (UKR)
- Milan (ITA)
- Newcastle United (ENG)
- Lazio (ITA)
- Real Sociedad (SPA)
- FC Copenhagen (DEN)
- RB Leipzig (GER)
- Napoli (ITA)
- Porto (POR)
- PSV (NED)
- Inter Milan (ITA)
UEFA2023/2024: A ina za a buga wasan karshe?
An shirya gudanar da wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na 2024 a ranar Asabar, 1 ga Yuni a filin wasa na Wembley, London, UK.
An dakatar da Ronaldo a Saudiya
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar gudanarwar wasanni ta kasar Saudiya ta dakatar da Cristiano Ronaldo daga taka leda na wasu kwanaki.
Wannan dakatarwar ta biyo bayan samun Ronaldo da karya dokar wasanni ta kasar a bangaren murna yayin da aka ci kwallo.
Ronaldo ya yi murna a wani yanayi na rashin da'a bayan zura kwallo a ragar kungiyar Al-Shabab.
Asali: Legit.ng