Jerin Tsofaffin ’Yan Wasan Najeriya 5 Masu Son Kujerar Peseiro Bayan Barin Kocin Super Eagles
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Tun bayan barin Jose Peseiro daga mukamin mai horas da ‘yan wasan Super Eagles, tsofaffin ‘yan wasan Najeriya sun nuna sha’awar mukamin.
Har ila yau, bayan ‘yan Najeriya da ke sha’awar mukamin, akwai kocin Portugal Antonio Conceicao da ya nuna sha’awar horas da tawagar.
Manyan tsofaffin ‘yan wasa biyar da suka taka rawar gani a gasar AFCON ta shekarar 1994 da kuma gasar kofin duniya a Amurka suna kan gaba a neman mukamin, cewar SportsBrief.
Wannan na zuwa ne bayan rufe karbar neman mukamin kocin Super Eagles da aka yi a ranar Talata 12 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta jero muku tsoffin ‘yan wasan da suka nuna sha’awar rike ragamar Super Eagles.
1. Emmanuel Amunike
Tsohon dan wasan Barcelona da Sporting SP ya nuna sha’awar neman kujerar bayan kwantiragin Jose Peseiro ya kare.
Amunike ya bugawa Najeriya wasanni har 27 inda ya zura kwallaye tara yayin da ya ke taka leda.
2. Daniel Amokachi
Tsohon dan wasan wanda aka haife shi a Kaduna yana daga cikin wadanda suka nuna sha’awar zama kocin Super Eagles.
Amokachi ya bugawa Najeriya wasanni da suka fafata a gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Faransa a shekarar 1998.
3. Sunday Oliseh
Oliseh ya taka leda a tawagar Super Eagles a matsayin dan wasan tsakiya wanda ya taka rawar gani, cewar BusinessDay.
Har ila yau, Oliseh ya buga wasanni 63 inda ya yi nasarar zura kwallaye uku, daga cikinsu akwai kwallon da ya ci Sifen a a gasar cin kofin duniya a 1998
4. Samson Siasia
Siasia ya taba rike mukamin kocin Super Eagles daga shekarar 2010 zuwa 2011 yayin da aka sake nada shi a 2016.
A shekarar 2019 ne hukumar FIFA ta dakatar da Siasia daga harkar wasanni kan zargin sayar da wasa.
5. Finidi George
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Enyimba na daga cikin masu neman zama mai horas da 'yan wasan na Super Eagles.
Finidi ya fara bugawa Najeriya wasa a shekara 1991 a gasar AFCON da aka buga da kasar Burkina Faso, cewar Pulse Sport.
Sauran masu sha'awar kocin Super Eagles
Sauran masu neman kujerar sun hada da kocin rikon kwarya na Super Eagles, Salisi Yusuf da Michael Nsien da Sylvanus Okpala.
Yanzu hukumar NFF ake jira ta dauki mataki a kan wanda zai jagoranci tawagar.
Peseiro ya bar aiki da Super Eagles
Kun ji cewa kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya ajiye mukaminsa bayan kwantiraginsa ta kare.
Peseiro ya jagoranci Super Eagles a gasar AFCON da aka gudanar a wannan shekara a kasar Ivory Coast.
Asali: Legit.ng