Jerin Kasashen Nahiyar Afrika 10 da Suka Fi Kowa a Jadawalin Hukumar FIFA Bayan Kallama Gasar AFCON
Kawanaki kadan bayan kammala gasar AFCON a kasar Ivory Coast, Hukumar FIFA ta cire jadawalin kasashe kamar yadda ta saba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Hukumar FIFA ta fitar da jadawalin ne a yau Alhamis 15 ga watan Faburairu wanda ya kunshi kasaseh da dama a duniya.
Jerin kasashen Afirka a jadawalin
Kamar yadda jadawalin ya ke, Najeriya ta kasance na uku yayin da kasar Ivory Coast da ta lashe gasar AFCON ta ke mataki na biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta jero muku jadawalin kasashen Afirka guda 10:
1. Morocco
Morocco ita ce ta farko a Nahiyar Afirka yayin da ta ke mataki na 12 a duniya baki daya bayan ta samu karin mataki daya.
2. Senegal
Kasar Senegal da Ivory Coast ta cire a gasar AFCON ta tsallako zuwa mataki na biyu yayin da ta ke mataki na 17 a duniya.
3. Najeriya
Bayan rasa nasara a wasan karshe a gasar AFCON, Najeriya ta samu nasarar kasancewa ta uku yayin da ta tsallako daga mataki na 42 zuwa 28 a duniya.
4. Masar
Masar ta yi rashin nasara inda ta sauko kasa inda yanzu ta ke mataki na hudu a Afirka yayin da ta ke mataki na 36 a duniya.
5. Ivory Coast
Duk da nasarar lashe gasar AFCON, Ivory Coast ta hauro mataki na biyar daga na 10 a Afirka yayin da ta ke mataki na 39 a duniya.
6. Tunisia
Kasar Tunisia ta kasance na shida a Nahiyar Afirka yayin da haura daga mataki na 54 zuwa na 41 a duniya.
7. Algeria
Algeria ita ce kasa da ke mataki na bakwai a Afirka yayin da samu koma baya a duniya inda ta ke mataki na 43.
8. Mali
Mali ita ce kasar ta takwas a Nahiyar Afirka yayin da ta samu karin girma a duniya inda ta ke mataki na 47.
9. Kamaru
Kasar Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya ta na mataki na tara a Afirka yayin da samu karuwa a duniya a mataki na 51.
10. Afirka ta Kudu
Kasar da Najeriya ta yi waje da ita a gasar AFCON ita ce ta 10 a Afirka yayin da ta ke mataki na 58 a duniya.
Sadiq ya gargadi ‘yan Najeriya
Kun ji cewa dan wasan gaban Super Eagles, Sadiq Umar ya gargadi masu caccakarsu bayan rashin nasara a AFCON.
Umar ya ce shi ba kaman Alex Iwobi ba ne da za su saka shi a gaba wurin sukarsa bayan kammala gasar.
Asali: Legit.ng