AFCON: Fitaccen Malamin Addini Ya Fadi Kasar da Za Ta Yi Nasara, Sai Dai Ya Ce Za a Tafka Kuskure

AFCON: Fitaccen Malamin Addini Ya Fadi Kasar da Za Ta Yi Nasara, Sai Dai Ya Ce Za a Tafka Kuskure

  • Yain da ake dakon wasan karshe a gasar AFCON, fitaccen Fasto a Najeriya ya yi hasashen wacce za ta yi nasara
  • Dakta Kan Ebube Muonso ya ce Ivory Coast za ta tafi da kofin gida sai dai hakan zai faru ne a cikin kuskure
  • Faston ya bayyana haka ne a shafin Facebook na cocinsa, Power and Victory a jiya Juma’a 10 ga watan Faburairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Shahararren Fasto, Dakta Kan Ebube Muonso ya yi hasashen kasar da za ta lashe gasar AFCON a gobe Lahadi 11 ga watan Faburairu.

Ebube ya ce kasar Ivory Coast za ta tafi da kofin gida sai dai hakan zai faru ne a cikin kuskure.

Kara karanta wannan

AFCON" 'Dan Najeriya ya yi hasashen sakamakon wasan karshe tsakanin Najeriya da Ivory Coast

Fitaccen malamin addini ya fadi kasar da za ta yi nasara a gasar AFCON
Fasto Ya Fadi Kasar da Za Ta Yi Nasara Tsakanin Najeriya da Ivory Coast. Hoto: MB Media, Fareed Kotb/Anadolu.
Asali: Getty Images

Mene Faston ke cewa kan wasan Najeriya?

Faston ya ce ya na ta addu’ar samun nasarar Najeriya a wasan inda ya ce karfin ikon ubangiji zai kwace kofin zuwa Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Kan ya bayyana haka ne a shafin cocinsa, Power and Victory in Christ na Facebook a jiya Juma’a 10 ga watan Faburairu.

Kan ya yi hasashen cewa Ivory Coast za ta lashe kofin ne a kuskure wanda hakan zai faru sanadin kuskuren alkalin wasa.

Abin da Faston ya hango a wasan

Har ila yau, ya kara da cewa Najeriya ita ce ta fi dacewa da kofin a wasan karshe da za a gudanar.

A cewarsa:

“Na hango kasar Ivory Coast ta dauki kofin bayan alkalan wasa sun nuna son kai, amma Najeriya ta fi dacewa da kofin.
“Sai dai zan karbi kofin daga Ivory Coast na mika shi ga Najeriya da karfin mulkin ubangiji a aikin da zan fara yi a gobe.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

“A wallafawar da zanyi a gaba bayan yin aikin ,za ku gane cewa akwai karfin ikon mulki a hannun ubangiji.”

Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon wasan karshe tsakanin Najeriya da kasar Ivory Coast mai masaukin baki.

Musa ya jagoranci addu’a

Kun ji cewa Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya jagoranci addu’a ga wadanda suka mutu yayin wasan Najeriya.

Musa bayan addu’ar ya yi alkawarin da yardar Allah za su dawo da kofin gida don wadanda suka mutu da sauran ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel