AFCON: ‘Dan Najeriya Ya Yi Hasashen Sakamakon Wasan Karshe Tsakanin Najeriya da Ivory Coast

AFCON: ‘Dan Najeriya Ya Yi Hasashen Sakamakon Wasan Karshe Tsakanin Najeriya da Ivory Coast

  • Hankula sun karkata kan wani 'dan Najeriya, wanda ya yi hasashen cewa Najeriya za ta doke Senegal a a cikin mintuna 90 a soshiyal midiya
  • Ya yada wani bidiyo inda ya tantance makomar Super Eagles tare da bayar da tabbacin cewa Najeriya za ta kaucewa karin lokaci
  • Najeriya za ta so sake yin nasara karo na hudu a gadar AFCON a ranar Lahadi yayin da za ta kara da mai masaukin baki Ivory Coast

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani 'dan Najeriya ya yi fice a dandalin soshiyal midiya bayan ya yi hasashen yadda karon Najeriya da Ivory Coast za ta kaya a wasan matakin rukuni.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa kafin wasan, mutumin ya yi nazarin karfin kungiyar tare da bayyana cewa Najeriya za ta yi nasara a cikin lokaci.

Kara karanta wannan

AFCON: Fitaccen malamin addini ya fadi kasar da za ta yi nasara, sai dai ya ce za a tafka kuskure

'Dan Najeriya ya yi hasashe kan gasar AFCON
AFCON: ‘Dan Najeriya Ya Yi Hasashen Sakamakon Wasan Karshe Tsakanin Najeriya da Ivory Coast Hoto: @thehindsightpod/TikTok
Asali: TikTok

A wani bidiyo da @thehindsightpod ya wallafa, ya ce yana da tabbacin cewa Najeriya ba za ta bukaci karin lokaci ko fenariti ba don yin nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu Najeriya za ta kara da mai masaukin baki Ivory Coast a wasan karshe a ranar Lahadi, tana mai fatan nasara a karo na hudu a gasar AFCON.

Tuni dai Najeriya ta doke Ivory Coast da ci 1-0 a matakin rukuni, wanda hakan ya bata dama kan abokan karawarta.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Ufiumarfaruk ya ce:

"Wannan mutumin dattijo ne jinjina yallabai."

Dynamic Range:

"Babban mutum!!"

Okeemegor:

"Cikakken lokaci Najeriya 2- 2 Ivory coast. Osimhen zai ci kwallo na uku amma za a soke 1. Wannan shine abin da na gani, zan dawo kan wannan bayan wasan. Oshimhen zai zura kwallo Najeriya za ta yi nasara kan fenariti."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

SportPremi:

“Ivory Coast 0-2 Najeriya.”

Malami ya fadi kasar da za ta ci gasar AFCON

A wani labarin, mun ji cewa shahararren Fasto, Dakta Kan Ebube Muonso ya yi hasashen kasar da za ta lashe gasar AFCON a gobe Lahadi 11 ga watan Faburairu.

Ebube ya ce kasar Ivory Coast za ta tafi da kofin gida sai dai hakan zai faru ne a cikin kuskure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel