AFCON: Tsohon Hadimin Buhari Ya Tuna Arangamarsa da Wani ‘Dan Obidient a Wasan Najeriya
- Hadimin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa kwallon kafa wani abu ne guda da zai iya haɗa 'yan Najeriya
- Ahmad ya bayyana cewa ya hadu da wani 'dan Najeriya a Bouake yayin wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a Cote D'Ivoire
- Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce shi da wasu 'yan Najeriya sun yi raha da daukar hotuna ba tare da tunanin banbancin siyasa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Tsohon hadimin Muhammadu Buhari, ya tuna arangamarsa da wani magoyin bayan Peter Obi, tsohon 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023.
A wani rubutu da ya yi a shafin X a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, Ahmad ya bayyana cewa kwallon kafa shine abu guda da zai haɗa 'yan Najeriya.
Bashir ya ce ya hadu da wani mutum a Bouake, wajen da aka buga wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a Cote D'Ivoire, kuma sun yi dariya da rungume juna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa bayan sun nuna farin cikinsu da daukar hotuna, mutumin ya bayyana masa cewa shi mai goyon bayan Peter Obi wanda aka fi sani da "Obidient".
Amma sai ga shi sun yi raha a tare saboda wasan kwallon kafa ne.
Yadda kwallon kafa zai iya haɗa kan 'yan Najeriya, Ahmad
Ahmad ya jaddada cewar nasarar Super Eagles kan Bafana Bafana na Afrika ta Kudu a wasan kusa da karshe na gasar AFCON ya sa gaba 'daya 'yan Najeriya sun nuna soyayyarsu ga kasar a karo na farko.
Ya ce:
"Watakila kwallon kafa shine kadai abin da zai iya hada kan kasar nan ba tare da la'akari da addini ko kabila ba. Na yi mamakin wani lamari na musamman da ya faru a Ivory Coast jiya.
"Bayan wasan, yayin da muke murna, wani ya tunkare ni yana ihun Najeriya cikin 'daga murya. Muka rungume juna sannan muka yi hotuna.
"Cikin rada, ya bayyana cewa shi 'dan Obidient ne, amma a irin wannan yanayi na nasara, mun hade sannan muka yi murnar nasararmu a tare.
"Abu kamar wasan daren jiya ne zai sanar da kai cewa cikin yanayinmu na musamman, duk muna tsananin son Najeriya."
Ga rubutun a kasa:
Shettima ya taya 'yan Eagles murna
A wani labarin kuma, mun kawo cewa ba a bar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a baya ba yayin murnar nasarar da Super Eagles ta samu.
Shettima ya shiga cikin 'yan wasan na Najeriya yayin da suke rawar murnar samun damar shiga wasan karshe a gasar AFCON.
Bidiyon ya matukar daukar hankali inda aka nuno su cikin annashuwa da walwala.
Asali: Legit.ng