AFCON 2023: Hanyoyi 3 da Tawagar Najeriya Za Ta Iya Doke Afrika Ta Kudu a Wasan Kusa da Na Karshe
- An bayyana hanyoyi uku da tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta iya doke tawagarBafana Bafana ta Afirka ta Kudu
- Kula da tsaron gida, sarrafa tsakiyar fili da kuma tabbatar da ba a je fagen bugun daga kai sai mai tsaron gida ba
- Tawagar Super Eagles za ta kara da tawagar kasar Afirka ta Kudu a filin wasa na La Paix a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
An ba tawagar Super Eagles ta Najeriya shawarar yadda za ta lallasa tawagar Bafana Bafana a wasan kusa da na karshe don tsallakewa zuwa wasan karshe na gasar cin kofin AFCON 2023.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Najeriya za ta iya doke Afrika ta Kudu a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu idan ta kula da wasu muhimman abubuwa guda uku.
Tsaron gida mai ƙarfi
Najeriya na iya tsallakewa zuwa wasan karshe idan karfafa tsaron gidanta wanda dama hakan ne ya sa aka zura musu kwallo daya kacal a wasanni biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum uku masu tsaron baya William Troost-Ekong, Semi Ajayi da Calvin Bassey za su kara kwazon su ta hanyar hana 'yan wasan hamayya wucewa.
Sarrafa tsakiya
Dole ne Frank Onyeka da Alex Iwobi dole ne su zage damtse tare da nuna basira a wasa da tawagar Afirka ta Kudu wadanda suka cika 'yan wasa a tsakiyar filin.
Karfin da Bafana Bafana ke da shi a tsakiyar fili na iya illata tsaron bayan Super Eagles ta hanyar kai hare-hare daga nesa.
Akwai yiyuwar mai horas da tawagar Najeriya, Jose Peseiro ya sauya tsarin sa na 3-4-3 da ya saba amfani da shi.
Samun nasara a cikin mintuna 90
Ya zama wajibi 'yan wasan Super Eagles na gaba, Victor Osimhen, Ademola Lookman da Moses Simon su tabbatar da nasarar Najeriya cikin mintuna 90.
Mai tsaron ragar tawagar Bafana Bafana, Rohwen Williams, ya kware a aikinsa kuma ya nuna hakan a wasanni hudu a jere sannan ya ture bugun fanareti hudu a haduwarsu da Cape Verde.
Zura kwallaye da cin nasara a wasan a ka'idajjen lokaci na mintuna 900 zai hana zuwa fagen bugun fanareti.
AFCON 2023: Bature ya yi hasashen makomar tawagar Najeriya
A wani labarin makamancin wannan, wani bature mai amfani da suna @callum_wm a manhajar TikTok ya ce Najeriya za ta yi nasara kan Afrika ta Kudu a wasan kusa da na karshe.
Baturen ya ce dan wasan Super Eagles, Chuka Iwobi ne zai zura kwallo ɗaya a ragar Bafana Bafana a wasan da za su buga gobe Laraba, 7 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng