AFCON 2023: Bature Ya Fadi Makomar Tawagar Najeriya a Wasan da Za Ta Buga da Afrika Ta Kudu

AFCON 2023: Bature Ya Fadi Makomar Tawagar Najeriya a Wasan da Za Ta Buga da Afrika Ta Kudu

  • Wani bature ya yi hasashen sakamakon wasannin kusa da na karshe da za a buga a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi
  • A wasan farko da ya hada Super Eagles ta Najeriya da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu, ya fadi sakamon wasan da dan wasan da zai zura kwallo a raga
  • Hasashen da ya yi na wasannin biyu bai yi wa wasu masoya kwallon kafa dadi ba, yayin da wasu kuma suka ba da nasu hasashen

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gabanin wasannin kusa da na karshe, wani bature ya yi hasashen kungiyoyin da za su kai ga wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) a ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda aka kashe naira biliyan 12 tare da cefanar da kadarorin Kotun Koli ba bisa ka'ida ba

A cikin wani faifan bidiyo na TikTok, @callum_wm ya ce wasan Najeriya da Afirka ta Kudu a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu zai kare ne da ci daya mai ban haushi.

Najeriya za ta lallasa Afrika ta Kudu
Bature ya ce Alex Iwobi zai zura kwallo a raga, wanda zai ba Najeriya nasara a wasan kusa da na karshe. Hoto: @callum_wm, X/(@Alookman_)
Asali: TikTok

Najeriya da Ivory Coast za su je wasan karshe

@callum_wm ya bayyana cewa Najeriya ce za ta yi nasara inda dan wasan Fulham Alexander Chuka Iwobi ne zai zura kwallo daya tilo a wasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wasa na biyu da ya kunshi Ivory Coast da DR Congo kuwa, @callum_wm ya ce za a kawo karshen wasan da ci biyu da nema.

Ya ce Nicolas Pepe ne zai zura kwallayen da tawagar Ivory Coast za ci.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun mayar da martani kan hasashen baturen:

Raja ya ce:

Kara karanta wannan

Ina sukar biyan da kudin fansa a baya, sai da aka sace ni na gane, tsohon shugaban DSS ya magantu

"Za ka sha mamaki."

Simply pc ya ce:

"Ubangiji ka amsa hasashen mutumin nan, tabbas muna fatan Najeriya ce za ta ci wasan."

User256 ya ce:

"Dr Congo za ta lashe kofin, ku dai tsaya nan kuna kallo."

Riri ya ce:

"Ba yadda za a yi mu yi nasara a kan SA da wannan mai tsaron gidan nasu a raga."

Mai tsaron ragar Afrika ta Kudu ya shirya karawa da Super Eagles

A wani labarin, mai tsaron ragar tawagar Afrika ta Kudu, Ronwen Williams ya ce ya shirya karawa da Super Eagles ta Najeriya a wasan kusa da na karshe.

A ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu ne za a buga wasannin kusa da na karshe a gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel