Uwar Gidan Shugaba Tinubu Ta Yi Ƙus-Ƙus da Matan Gwamnoni a Aso Villa, Bayanai Sun Fito

Uwar Gidan Shugaba Tinubu Ta Yi Ƙus-Ƙus da Matan Gwamnoni a Aso Villa, Bayanai Sun Fito

  • Mai ɗakin shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Bola Tinubu, ta gana da matan gwamnonin jihohi 36 a birnin tarayya Abuja
  • Wannan zama na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fama matsin rayuwa da tsadar kayayyaki sakamakon karyewar darajar Naira
  • A wurin taron, matar Tinubu ta jero kudirinta na tsoma hannu a ɓangarori da dama da suka haɗa da ilimi, kiwon lafiya, noma da tallafawa mata a 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Uwar gidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta gana da matan gwamnonin jihohin kasar nan a fadar shugaban ƙasa da ke birnin Abuja.

A wurin wannan taro, uwar gidan shugaban ƙasa ta bayyana aniyar tsoma hannu domin inganta harkokin noma, kiwon lafiya da kuma ilimi a shekarar 2024.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kai farmaki wurin taron murnar nasarar gwamnan PDP a Kotun Ƙoli, sun tafka ɓarna

Matar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu.
Uwar Gidan Shugaba Tinubu Ya Gana da Matan Gwamnoni a Villa, Bayanai Sun Fito Hoto: Oluremi Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa matar Shugaba Tinubu ta kuma yi tsokaci kan ajendar taimaka wa mata da tallafi a wannan shekara da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin matar Tinubu yayin ganawa a Villa

Da take jawabi a taron, Oluremi Tinubu ta ba da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za a kawo karshen wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta na yunwa da ƙunci tare da manufofi na gari.

Ta kuma jaddada cewa 2024 cike take da "zaman lafiya, ci gaba, wadata da kuma manyan nasarori" domin amfanin 'yan Najeriya baki daya.

Misis Tinubu ta yabawa matan gwamnonin bisa jajircewa da goyon bayan da suka bayar a 2023, inda ta bukace su da kada su yi kasa a gwiwa wajen magance bukatun marasa galihu a jihohinsu.

A ruwayar Vanguard, matar shugaban kasar ta ce:

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan buƙatar magoya bayan gwamnan PDP da ake zargi da ta'addanci

"Lokaci irin wannan mai wahala yana buƙatar tunani mai zurfi, don haka dole ne mu haɗu wuri ɗaya. Bugu da ƙari, yanayin wahala na ɗan lokaci ne, ba da daɗewa ba zai shuɗe.

Ta kara da cewa shirin tallafawa manoma mata (WASP) zai tallafi kuɗi ga manoma 20 daga jihohi 5 da su daga jihohi 5 na Kudu maso Yamma.

Kotu ta hana belin mutum 5 a arzikin

A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan buƙatar belin magoya bayan Gwamna Fubara na jihar Ribas kan tuhumar ta'addanci.

Mutanen 5 da aka kama na fuskantar shari'a kan tuhume-tuhume bakwai da suka samo asali daga ƙona wani sashin majalisar dokokin Ribas

Asali: Legit.ng

Online view pixel