Matasa Sun Kona Hoton Davido a Maiduguri, Sun Nemi Ya Ba Da Hakuri Kan Bidiyon Cin Mutuncin Addini

Matasa Sun Kona Hoton Davido a Maiduguri, Sun Nemi Ya Ba Da Hakuri Kan Bidiyon Cin Mutuncin Addini

  • Matasa a Maiduguri sun kona wani babban hoton na mawaƙin kudancin Najeriya Davido
  • Matasan sun nemi Davido ya goge bidiyon sannan kuma ya bai wa Musulmin Najeriya haƙuri
  • Tuni dai mawaƙin ya goge bidiyon mai daƙiƙu 45 da biyar da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan shan suka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Maiduguri jihar Borno - Wasu matasa a Maiduguri babban birnin jihar Borno, sun fito kan titi don nuna fushinsu kan bidiyon da mawaƙi Davido ya wallafa a shafinsa na Twitter cikin 'yan kwanakin nan.

Mawaƙin ya sha suka biyo bayan ɗora wani bidiyo da bai yi wa Musulmin Najeriya daɗi ba.

A cikin bidiyon, wanda wani mai suna Sultan ya wallafa a shafinsa na Twitter, matasan sun nemi Davido da ya fito ya bai wa Musulmin Najeriya haƙuri.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sanya Dole Shugaba Tinubu Ya Bayyana Sunayen Ministocinsa Nan Da Ranar Juma'a

Matasa sun ƙona hoton Davido a Maiduguri
Matasa sun bankawa hoton Davido wuta a Maiduguri, sun nemi ya ba da haƙuri. Hoto: @Davido, @Sarki_sultan
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me bidiyon na Davido ya ƙunsa? Ƙarin bayani

Davido dai ya ɗora wani ɓangare ne na bidiyon wani sabon mawaƙi daga cikin yaransa, mai suna Logos Olori na wata waƙa da ya sanyawa suna 'Jaye Lo'.

Sai dai hakan ya janyo suka da cece-kuce daga wurin Musulman Najeriya da dama saboda nunowa da aka yi an haɗa sallah da rawa a cikin bidiyon.

Wasu daga cikin shahararrun Musulmai ciki kuwa har da jarumin Kannywood Ali Nuhu, da tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Buhari, Bashir Ahmad, sun nemi Davido ya goge bidiyon sannan ya ba da haƙuri.

Davido ya goge bidiyon bayan shan kakkausar suka

Sai dai mawaƙin bayan shan kakkausar suka, ya amsa kiraye-kirayen da ake yi masa inda ya goge bidiyon daga shafin nasa na Twitter.

Sai dai duk da goge bidiyon da mawaƙin ya yi, matasan na Maiduguri ba su gamsu ba inda suka nemi ya fito ta kafafen sada zumunta ya nemi afuwar al'ummar Musulmin Najeriya.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Litar Man Fetur Za Ta Dawo Naira 50 Kacal a Najeriya, Fitaccen Malami Ya Faɗi Gaskiya

@Sarki_sultan da ya wallafa bidiyon a Twitter ya ce Davido ya fito kawai ya ba da haƙuri, ya ce ba wani abu ba ne don ya yi haka.

“Ba ma wasa da Sallah”, Ali Nuhu ya yi martani kan bidiyon Davido

A baya Legit.ng ta wallafa muku cewa jarumin Kannywood Ali Nuhu ya bi sahun Musulmin Najeriya wajen sukar bidiyon waƙar da Davido ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Tsohon Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ne ya fara yin Allah wadai da bidiyon a shafinsa na Twitter kafin daga bisani Ali Nuhu ya wallafa nasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel