Mulkin Tinubu: Wani Malami Ya Ce Litar Man Fetur Za Ta Dawo Naira 50 a Najeriya

Mulkin Tinubu: Wani Malami Ya Ce Litar Man Fetur Za Ta Dawo Naira 50 a Najeriya

  • Wani malamin addini a jihar Legas, Prophet Elijah Bamidele, ya faɗi labari mai daɗi ga yan Najeriya yayin da man fetur ya ƙara tsada
  • Fastor Bamidele ya ce shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu, ne kaɗai mutumin da zai iya gyara Najeriya
  • Malamin Majami'ar ya kuma bayyana cewa litar Fetur da ake sayar wa yanzu N617, ba da jima wa ba zata faɗi warwas ta koma N50

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Fitaccen Malamin addinin kirista a Najeriya, Prophet Elijah Bamidele, na cocin Christ House of Prayer and Deliverence ya tabbatar da 'yan Najeriya na shan wahala.

Malamin ya ce baki ɗaya mutanen ƙasar nan, ko mutum ya zaɓi shugaba Bola Tinubu ko bai zaɓe shi ba, yana fama da wahalhalun rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.

Prophet Elijah Bamidele da Bola Ahmed Tinubu.
Mulkin Tinubu: Wani Malami Ya Ce Litar Man Fetur Zata Dawo N50 a Najeriya Hoto: Prophet Elijah Bamidele, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sai dai malamin ya ƙara da cewa bayan wuya sai daɗi domin, "Zinare ba ya sarrafuwa sai ya biyo ta cikin wuta sannan ya zama abin ƙawa."

Kara karanta wannan

‘Ba Batun Neman Minista Ba Ne’, Jonathan Ya Bayyana Dalilin Kai Wa Tinubu Ziyara

Ku ƙara hakuri da mulkin shugaba Tinubu - Fastor Bamidele

Bamidele ya ƙara kwantar wa yan Najeriya hankali kana ya buƙaci su ƙara hakuri domin, "Nan gaba akwai lokacin da duk waɗanda suka bar ƙasar nan zasu ƙaunaci dawowa gida."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babban malamin ya yi nasiha a kan fata mai kyau yayin da yake wa'azi ga mabiyansa a coci kwanan nan, rahotanni sun tabbatar da haka.

Litar man fetur zata sauko zuwa N50

A kalamansa, Malamin ya ce:

"Na tambayi Allah yayin da nake Addu'a cewa 'Meyasa muka shiga wannan yanayin? Allah ya bani amsa da cewa 'Ka zama mai haƙuri ɗa na'. Mutum ɗaya da zai iya gyara ƙasar nan shi ne Bola Ahmed Tinubu."
"Akwai lokacin da zai zo wannan tsadar fetur da muke ta kuka a kansa, zamu riƙa sayen shi kan N50 a kowace lita a ƙasar nan tamu."

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: An Bayyana Mutanen Da Shugaba Tinubu Zai Naɗa a Matsayin Ministoci Kwanan Nan

"Dala da muke ta ɓaɓatu a kanta, zata dawo daidai da Naira ɗaya. Ba zan matsa muku dole ku amince da magana ta ba amma dai ina gaya muku abinda zai faru nan gaba."

Jami'an DSS Sun Sake Kama Dakataccen Gwamnan CBN

A wani labarin na daban kuma Jami'an DSS sun sake damƙe tsohon gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele bayan kammala zaman Kotu a Legas.

Hakan ya biyo bayan taƙaddama da rikicin da ya auku tsakanin dakarun DSS da jami'an hukumar kula da gidajen gyaran hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel