Duk da Albashin Naira Biliyan 2 a Wata, Akwai ‘Dan Wasa 1 da Ya Sha Gaban Ronaldo a Kudi

Duk da Albashin Naira Biliyan 2 a Wata, Akwai ‘Dan Wasa 1 da Ya Sha Gaban Ronaldo a Kudi

  • Cristiano Ronaldo zai samu makudan biliyoyin kudi da ya koma buga kwallon kafa a Saudi Arabia
  • Duk da £173m da tauraron zai rika karba, Faiq Bolkiah ba zai iya kamo wanda bai yi suna a kwallo ba
  • A tarihin Duniya, ba ayi ‘dan wasan da zai karbi irin albashin tsohon ‘dan kwallon na Manchester ba

Saudi Arabia - Abin da Cristiano Ronaldo zai rika karba a shekara a matsayin albashi a kungiyar Al Nassr a Saudia Arabiya shi ne Dala miliyan £62m.

Jaridar Sun ta ce duk da tulin wannan kudi da ‘dan kwallon kafan zai rika samu a kasar Saudi Arabia, ba shi ne ‘dan wasan da ya fi kowa dukiya ba.

Kafin kwantiraginsa ya kare a 2025, duk shekara Ronaldo zai rika karbar £173m idan aka hada da kudin talla da sauran hakkokin da zai rika tashi da su.

Kara karanta wannan

Mutum 6m: Zuwan Ronaldo ya jawowa kulob din Saudiyya farin jini, jama'a sun yi tururwa a Instagram

Wannan kwantiragi ya sa tauraron ya samu kwangilar da ta fi kowace tsoka a tarihin Duniya. A kudin Naira, Ronaldo zai rika samun N2.7bn a shekara.

Gaba da gabanta, Faiq Bolkiah da CR7

Duk maganar da ake yi, Faiq Bolkiah wanda ya gagara tabuka abin kwarai a kungiyar Leicester City ta kasar Ingila, ya dama Ronaldo a maganar arziki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yanzu haka Faiq Bolkiah mai shekara 24 ya koma kasar Thailand yana taka leda. Kafin nan ya yi yunkurin bugawa kungiyoyin Arsenal da Chelsea.

Cristiano
Cristiano Ronaldo da motocinsa Hoto: www.financialexpress.com
Asali: UGC

Rahoton ya ce ‘Dan wasan ya fito daga gidan sarautar Brunei, kuma yana da gado a dukiyar £13bn da Mai martaba Hassanal Bolkiah ya mallaka a Duniya.

Ana lissafin abin da ‘dan kwallon ya mallaka ya nunka na Ronaldo kimanin sau 15 a halin yanzu.

Facakar Faiq Bolkiah da dukiya

Kara karanta wannan

Da Duminsa: PSC ta Dakatar da Jami’in da Ya Harbe Lauya Mai Ciki a Legas

Jaridar Dailystar tace akwai lokacin da Bolkiah yake kashe £35m wajen harkar motoci, gwala-gwalai da kuma cashewa da ‘yan mata a kowane wata.

Amma idan ana maganar buga kwallon kafa, Bolkiah ba sa’an tsohon ‘dan wasan na Manchester United ba ne wanda ya lashe Ballon D’or har sau biyar.

Shi Bolkiah ya fara wasa ne da kungiyar AFC Newbury kafin ya sa hannu a wani kwantiragin shekara daya da Southampton a kasar Ingila a 2009.

Daga nan Chelsea ta jarraba ‘dan wasan yana matashi, kafin nan Arsenal tayi kokarin daukar shi. Ana haka ne Leicester ta saye shi a karshen kakar 2015.

Attajirin bai iya yin suna a Leicester ba duk da nasarar da aka samu a gasar Firimiya bayan zuwansa. Yanzu haka ya bugawa kasar Brunei wasanni shida.

Ronaldo ya yabi Messi

A wani jawabi da ya yi a Twitter, an ji labarin yadda Ronaldo Luis Nazario de Lima ya yabi 'dan wasa Lionel Messi wanda shi ne Kyaftin din kasar Argentina.

Kara karanta wannan

Ma’aikata Sun Bada Sharadi Kan Karin Albashi, Sun ce ba Shi Kadai Ake Bukata ba

Ronaldo yana ganin ‘Dan wasan mai shekara 35 ya ba marada kunya, ya yi kwallon da babu wanda zai iya yi masa adawa a gasar cin kofin Duniya na 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel