Gwani ya ga gwani: Ronaldo Ya Aikawa Messi Sako Bayan Nasarar Argentina a Qatar

Gwani ya ga gwani: Ronaldo Ya Aikawa Messi Sako Bayan Nasarar Argentina a Qatar

  • Ronaldo Luis Nazario de Lima ya yi magana a shafin Twitter da Argentina ta ci gasar kofin Duniya
  • Tsohon gwarzon ya yabi Lionel Messi wanda ya jagoranci kasarsa zuwa ga nasara a kan Faransa
  • A yayin da Duniya take taya Messi murna, abokin karawarsa, Cristiano Ronaldo bai ce uffan ba tukun

Qatar - Ronaldo Luis Nazario de Lima ya na cikin wadanda suka fito suka taya Lionel Messi murna a sakamakon nasarar da Argentina ta samu.

Tsohon ‘dan wasan kasar Brazil, ya yabi ‘dan wasan gaban kasar Argentina bayan sun doke Faransa a bugun finariti a gasar kofin Duniya.

Wani rahoto na Eurosport ya ce Ronaldo Luis Nazario de Lima yayi magana a Twitter, ya ce Messi mai rike da kambun Argentina, ‘dan baiwa ne.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 7 da Wallafar Hasashen Nasarar Messi, Lamarin Ya Faru Kuma Jama'a Sun Yi Caa kan Mutumin

Ronaldo wanda ya ci zamaninsa tsakanin 1990 zuwa 2011 ya ce kwallon da Messi ya buga a gasar kofin Duniyan ya fi karfin a iya yi masa adawa.

Messi ya bar tarihi

A kowane zagaye, sai da ‘dan wasan na PSG ya zura kwallo. Wannan ne karon farko da wani ya yi haka a gasar, ya kare da kwallaye bakwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lionel Messi
Lionel Messi a Qatar Hoto: AFP
Asali: AFP

Irin wannan kwallon ya fi karfin adawa. Na ga ‘Yan Brazil da mutane daga duk kasashen Duniya suna kiran sunan Messi a kayataccen wasan karshen.
An yi sallama mai daraja da tauraron da bayan zamansa gwarzon gasar cin kofin Duniya, ya jagoranci zamani. Ina taya ka murna, Lionel Messi.

- Ronaldo

Shi karon kan shi Ronaldo ya jagoranci kasarsa ta Brazil wajen samun irin wannan nasara a gasar 2002 da aka buga a kasashen Koriya da Jafan.

Kara karanta wannan

WC 2022: Abin da Tinubu, Atiku da Kwankwaso Suka Fada kan Argentina, Messi

A gasar bana da aka yi a kasar Qatar, Messi ya zura kwallaye biyu a wasan karshe yayin da Kylian Mbappe ya jefawa Faransa kwallaye har uku.

Ina Cristiano Ronaldo?

Daily Mail ta ce shi kuma Cristiano Ronaldo wanda ya fi kowa yawan mabiya a Duniya bai ce uffan ba tun da Argentina ta doke Faransa a jiya.

Ronaldo ya bar Qatar yana kuka da Portugal ta sha kashi a hannun kasar Morocco. Ana sauraron mai zai fada a Twitter, Facebook ko Instagram.

Atiku, Kwankwaso sun yi magana

Rahoto ya zo cewa Atiku Abubakar ya ce za a dauki darasi daga rayuwar Lionel Messi ganin kasar Argentina ta doke Faransa a bugun Finariti.

Shi kuma Bola Tinubu ya ce Messi shi ne Emi lo kan a gasar da aka buga a kasar Larabawan, Rabiu Kwankwaso yana ganin wasa ya yi armashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel