Ma’aikata Sun Bada Sharadi Kan Karin Albashi, Sun ce ba Shi Kadai Ake Bukata ba

Ma’aikata Sun Bada Sharadi Kan Karin Albashi, Sun ce ba Shi Kadai Ake Bukata ba

  • Kungiyoyin ‘yan kasuwa da ‘yan kwadago sun yi magana a kan karin albashin da ake cewa za ayi
  • Wani jagora a kungiyar NLC ya ce dole a fara duba tsadar rayuwa da karyewar da Naira take yi
  • Sakataren TUC ya bada makamanciyar wannan shawara, ya ce N30, 000 da ake biya ya yi kadan

Abuja - Kungiyoyin ‘yan kwadago na kasa watau NLC da TUC ta ‘yan kasuwa ta jero sharuda a game da karin albashin da ake shirin yi a Najeriya.

Punch ta rahoto kungiyoyin su na cewa ya zama wajibi a duba matsalar tashin farashin kaya da karyewar Naira kafin gwamnati tayi karin kudi.

‘Yan kwadagon sun ce farashin kusan komai tashi yake yi a kasar nan, idan aka cigaba da tafiya a haka, babu karin da zai iya biya bukatun ma’aikata.

Kara karanta wannan

Kila CBN Ya Canza Shawara, Sanatoci Sun Ce a Ajiye Batun Canjin Kudi Sai Yunin 2023

Mataimakin shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ya shaidawa jaridar cewa N30, 000 ba zai isa a saye kananzir, man fetur da gas na tsawon wata daya ba.

Komai ya kara kudi a yau - NLC

"Maganar da ake yi, farashin kananzir, litar man fetur da gas da za a saya a kwanaki 30 ya fi karfin mafi karancin albashin N30, 000 da ake biya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saboda haka ba maganar adadin kudin da za a biya ba ne, ko nawa za a bada ba zai iya magance matsalar mu ba, dole a duba tashin farashin kaya.
Idan ba haka ba kuwa, a kwana ko biyu, duka kudin za su kare." - Joe Ajaero
Ma’aikata
Zanga-zangar Ma'aikatan Najeriya Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin da ya kamata gwamnati ta duba - TUC

Ajaero ya ce ba za a iya fadan nawa ya kamata a biya ma’aikatan ba, sai kwamitocin da abin ya shafa sun zauna, sun duba halin tattalin arzikin kasa tukun.

Kara karanta wannan

Abin nema: Majalisa ta amince da bukatar Buhari, zai sake runtumo bashi mai yawa

Kwamitin ya kunshi ‘yan kwadago, ma’aikata da bangaren gwamnati da suke da ta-cewa a lamarin, sai dukkaninsu su na nan sannan za a tsaida magana.

Shi ma Sakatare Janar na TUC, Nuhu Toro ya ce ana bukatar gwamnati ta tsoma baki a kan farashin kaya a Najeriya, sannan a duba yadda Naira take karyewa.

An rahoto Nuhu Toro yana cewa karin albashi kadai ba zai isa ba, ya bada misali da ya nuna ko a kudin mota, N30, 000 din da ake biyan ma’aikata za su kare.

A karshe babu kudin kiwon lafiya, abinci da kuma kula da yara, Toro ya ce ba za su bari a tafi a haka ba, a matsayinta na kungiya, TUC za ta sa baki a lamarin.

Za a kara albashi a 2023?

NLC da TUC sun yi magana ne bayan jin labarin Dr. Chris Ngige yana cewa ma’aikata da jami’an gwamnatin tarayya su saurari karin albashin da za ayi a badi.

Kara karanta wannan

Ngige: Gwamnati na Duba Albashin Ma’aikata, Akwai Yiwuwar Ayi Karin Kudi a 2023

Da ya zanta da manema labarai, Ministan kwadago da samar da aikin yi a Najeriya ya yi magana karir albashi da kudin ASUU na watanni 8 da aka ki biya.

Ngige ya kira 2022 da shekarar rigima da ‘yan kwadago ganin tataburzarsu da malaman jami’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel