Cristiano Ronaldo Ya Samu Kulob da Zai Koma, Zai Iya Tashi Da €400m a Shekaru 2
- Kungiyar Al-Nassr ta shiga cikin masu yin zawarcin Cristiano Ronaldo wanda a halin yanzu bai da kulob
- Idan zai buga mata kwallo na shekaru biyu da rabi, Al-Nassr za ta kashewa Ronaldo €400m nan da 2025
- Babu tabbacin cewa ‘dan wasan mai shekara 37 ya shirya barin nahiyar Turai, ya koma kasashen Larabawa
Qatar - Rahotanni na zuwa cewa tsohon ‘dan wasan gaban Manchester United, Cristiano Ronaldo yana kan gabar komawa Al-Nassr da buga wasa.
A wani rahoto da jaridar Marca ta fitar, an ji cewa kungiyar ta Al-Nassr da ke kasar Saudi Arabiya ta ba babban ‘dan wasan kwangila na shekara biyu.
Kungiyoyin kasashen Amurka suna neman sayen ‘dan wasan idan har ya yarda ya bar Turai, ana haka ne sai Al-Nassr ta nuna sha’awar ‘dan kwallon.
Kungiyar za ta biya Ronaldo €400m idan ya yarda ya buga mata wasa har zuwa shekarar 2025. A shekara idan aka yi lissafi, yana da akalla N91.2bn.
Ronaldo zai hadu da Ospina?
Jaridar Goal.com tace idan ‘dan wasan na kasar Portugal ya karbi tayin Al-Nassr, zai hadu da David Ospina wanda ya taba bugawa kungiyar Arsenal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
David Ospina shi ne mai tsaron ragar Arsenal ta kasar Ingila tsakanin shekarar 2014 zuwa 2019.
Babu mai sayen Ronaldo a Turai?
A halin yanzu tsohon ‘dan wasan na Real Madrid da Juventus yana kasar Qatar inda ake buga gasar cin kofin Duniya, kasarsa ta isa zuwa zagaye na gaba.
Masu nazarin kwallo su na tunanin Chelsea ba ta da sha’awar sayen ‘dan wasan – Haka zalika kungiyar Newcastle da take hannun Larabawan Saudiya.
Shugaban kungiyar Bayern Munich, Oliver Kahn ya nesanta kulob dinsu da tauraron Duniyan.
Eurosport tace duk shekara, Cristiano Ronaldo zai samu £172.9m a kungiyar kwallon kafan Larabawan da tayi shekaru uku ba ta ci gasar kasar Saudi ba.
Wata hira da Ronaldo ya yi, inda aka ji ya soki Erik ten Hag da yadda ake tafiyar da Manchester United tayi sanadiyyar da kungiyar ta katse kwantigarinsa.
An yaudare ni - Ronaldo
An ji labari Cristiano Ronaldo ya soki Manchester United, ya koka kan yadda ake gudanar da abubuwa a kungiyar, yace babu wani cigaban da aka samu.
Ronaldo ya zargi kocinsa da rashin girmama shi, sannan kuma ya maidawa tsofaffin abokansa irinsu Wayne Rooney martani saboda yawan sukarsa da suke yi.
Asali: Legit.ng