An yaudare ni: Ronaldo Ya yi Kaca-kaca da Kungiyarsa da Kocin Man Utd a Hira Mai Zafi

An yaudare ni: Ronaldo Ya yi Kaca-kaca da Kungiyarsa da Kocin Man Utd a Hira Mai Zafi

  • ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo ya soki Manchester United a wata hira da Piers Morgan ya yi kwanan nan
  • Tauraron ya koka kan yadda ake gudanar da abubuwa a kungiyar, yace babu wani cigaban da aka samu yanzu
  • Ronaldo ya zargi kocinsa da rashin girmama shi, sannan kuma ya maidawa irinsu Wayne Rooney martani

Manchester - A wata hira da ya yi da Piers Morgan, ‘dan wasan gaban Manchester United, Cristiano Ronaldo ya yi bayanin halin da ya tsinci kan shi.

Jaridar Sun ta fitar da labarin hirar da Piers Morgan ya yi da Cristiano Ronaldo a shirinsa na TalkTV, a nan aka ji ya soki kungiyar da yake bugawa wasa.

Ronaldo ya yi ikirarin abubuwa ba su tafiya daidai a kulob din tun da Sir Alex Ferguson ya ajiye aiki a 2013, ya kuma ce bai ganin girman Eric Ten Haag.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya yi babban kamu, an daura aurensa da diyar tsohon shugaban Amurka Trump

Skysports ta rahoto ‘Dan wasan mai shekara 37 a Duniya yana cewa kocin kungiyar watau Erik ten Hag bai ganin darajarsa, don haka shi ma bai girmama sa.

Wasu ba su son gani na - Ronaldo

A game da yunkurin korarsa daga kulob din, Ronaldo yace bayan mai horas da ‘yan wasan kungiyar, akwai mutum biyu ko uku da ke neman ganin bayansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Maganar gaskiya, ban sani ba. Bai dame ni ba. Mutane su ji gaskiyar lamari. Kwarai, ina jin an ci amana ta. Wasu ba su so na, ba a bana ba, har a bara.”
Ban san meyasa hakan yake faruwa ba. Tun da Sir Alex Ferguson ban ga canjin da aka samu ba, babu komai.

An kori Solskjaer, an dauko hayar Darekta

Misali, abin mamaki ne Man United ta sallami Ole (Solskjaer), ta kawo Ralf Rangnick, mutumin da ba koci ba ne, wannan ya daurewa kowa kai.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Sha Suka Saboda Hirarsa Da Sarkin Ingila Charles III

- Cristiano Ronaldo

Cristiano
Cristiano Ronaldo da Ten Haag Hoto: www.express.co.uk
Asali: UGC

Feguson, Rooney da Dawowa Manchester

‘Dan wasan na kasar Portugal yake cewa kaunar da yake yi wa Manchester United ta sa ya dawo kulob din, ya ki yarda ya tafi kungiyar Manchester City.

Nayi aiki da abin da zuciyata take so. Shi Sir Alex Feguson yace mani, ‘Ba za ta yiwu ka tafi Manchester City', sai na ce ‘To, ‘Yallabai.’

- Cristiano Ronaldo

A hirar, Ronaldo yace watakila Wayne Rooney yana sukarsa ne saboda shi ya daina kwallo, kuma ga shi idan aka yi maganar kyau, shi kyakkyawa ne.

Shari'ar Greenwood a Ingila

A karshen Oktoban bana ne aka ji labari ‘Dan wasan kwallon gaban kungiyar Manchester United, Mason Greenwood zai bayyana gaban kuliya.

Ana tuhumar Greenwood mai shekara 21 da laifin fyade, don haka zai kare kan shi a wata kotu mai zama a Salford a garin Manchester a kasar Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel