Umurnin Kai Shi Kurkuku: Shugaban Yan Sanda Nigeria Yayi Martani

Umurnin Kai Shi Kurkuku: Shugaban Yan Sanda Nigeria Yayi Martani

  • Shugaban Hukumar Yan Sandan Nigeria Usman Alkali Baba Ya Magantu Kan Hukunci kai Gidan Kaso
  • Hukumar Yan sanda Nigeria Bata ta ba sabwa umarni ko hukunci kotu wanda ta yanke ko ta zartar
  • Wata Kotu a Abuja tayi Umarnin kama Shugaban Hukumar Yan Sandan Nigeria

Abuja: Rundunar ‘yan sandan Najeriya na son bayyana cewa ofishin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba, psc(+), NPM, NEAPS, fdc, CFR, bai yi watsi da umarnin kotu ko kin bin doka da oda ba kamar yadda wata Kotu ta fada ba.

wannan ya Fito ne dai a kan batun da aka rika yadawa a kafafen yada labarai cewa IGP din ya bijirewa umarnin kotu na maido da wani jami’in rundunar da aka kora.

tsaro
Shugaban Yan Sanda Nigeria Yace Bazai Sabawa Umarnin Kotu Ba
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Bada Umarnin Jefa IGP na Yan Sanda Gidan Yari

Yana da kyau a lura cewa lamarin ya shafi wani jami’in da aka kora tun a shekarar 1992, shekaru kadan bayan IGP na yanzu ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya, bisa la’akari da hujjojin da aka samu da kuma rahotanni.

An yanke hukunci na baya-bayan nan game da lamarin a shekarar 2011 wanda bai kamata ya kasance karkashin kulawar hukumar ta rundunar ta yanzu ba. Don haka, labarin yana da ban mamaki Da rudarwa.

Mai Ya Janyo Batun

Sai dai IGP din ya umurci kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashin shari’a na rundunar da ya binciki zargin da ake yi masa a kokarinsa na tabbatar da matsayin kotun da kuma ba da shawara ta fuskar shari’a domin IGP ya gaggauta daukar matakin da ya dace.

Sufeto-Janar na ‘yan sanda ya jaddada kudirin sa na bin doka da oda tare da hada kai da bangaren shari’a don tabbatar da gaggauta aiwatar da shari’a don inganta tsarin shari’ar laifuka.

wannan Sanarwa dai ta fito ne ta bakin kakain rundunar Yan sandan na Kasa wato CSP OLUMUYIWA ADEJOBI, mnipr, mipra ta kafar Twitter din hukumar daga Babban ofishin yan sandan da ke Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel