Za Ayi Shari’a da ‘Yan Wasan Man Utd da PSG kan Zargin Fyade da Rashin Gaskiya

Za Ayi Shari’a da ‘Yan Wasan Man Utd da PSG kan Zargin Fyade da Rashin Gaskiya

  • ‘Dan wasan kwallon gaban kungiyar Manchester United, Mason Greenwood zai bayyana gaban kuliya
  • Ana tuhumar Mason Greenwood mai shekara 21 da laifin fyade, don haka zai kare kan shi a kotun Ingila
  • Haka zalika za a zauna da Neymar da tsofaffin shugabannin Barcelona da Santos a kotun a kasar Sifen

England- Ana tuhumar ‘dan wasan kwallon kafan Manchester United, Mason Greenwood da zargin aikata fyade da wasu munanan laifuffuka.

Rahotanni daga BBC sun tabbatar da cewa an shigar karar ‘dan wasan gaban Ingilan ne a wani kotun majistare da ke zama a Salford a kasar Birtaniya.

A ranar Litinin Mason Greenwood mai shekara 21 zai bayyana a gaban Alkali domin ya kare kansa daga zargi uku da wata Baiwar Allah take yi masa.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Gwamnatin Tarayya Ta Saki ‘Yan Boko Haram 100 Daga Kurkuku a Boye

Tun a watan Junairun 2022 aka tsare ‘dan wasan kwallon kafan bayan hotuna da bidiyo sun bayyana, ana zarginsa da cin zarafin wata budurwarsa.

‘Yan sandan garin Manchester sun yi ram da tauraron wanda hakan ya jawo aka daina sa shi a wasa, tun lokacin Ingila ba ta kara kiran shi kwallo ba.

Man Utd da PSG
Neymar Jr. a wasan Man Utd da PSG Hoto: www.neymarjr.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shari'ar Neymar ta taso

A wani rahoton da muka samu daga Mirror, mun ji cewa a goben ne kuma za a soma shari’a a kotu a kan tashin Neymar Jr. daga Santos zuwa Barcelona.

Rahoton yace wani kamfani mai suna DIS ya shigar da kara a kotu a kan cinikin da aka yi tsakanin kungiyar Santos na kasar Brazil da Barcelona a Sifen.

DIS ne yake da mallakin 40% na hakkokin ‘dan wasan a lokacin yana Santos, kamfanin yana zargin an boye gaskiyar kudin da aka saida Neymar.

Kara karanta wannan

Sunan Darektan Kamfe a APC Ya Fito a Kwamitin Yakin Neman Zaben Peter Obi

Lauyoyin DIS sun ce Neymar, Barcelona da Santos sun yi karya da suka ce fam miliyan €57 aka saida ‘dan kwallon, suna zargin farashin ya haura €80m.

Neymar zai iya tafiya gidan yari?

A dalilin wannan za ayi shari’a da Sandro Rosell, Josep Maria Bartomeu, Odilio Rodrigues Filho, Neymar da mahaifinsa a wani kotu da ke kasar Turai.

France 24 tace idan aka samu ‘dan wasan na PSG da laifi, zai iya shafe shekaru biyu a gidan yari da tarar $9.7m. Paulo Nasser shi ne lauyan da ya shigar da karar.

Za a je kotu a Oktoba

Kwanaki kun ji labari Sandro Rosell da Josep Maria Bartomeu za su amsa tambaya a game da cinikin tauraron da aka yi daga Santos zuwa Barcelona tun a 2013.

Ana zargin an aikata ba dai-dai ba wajen wannan ciniki, don haka ake zargin wadanda ake tuhuma da laifin hana kamfanin na DIS cikakken hakkinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel