Cinikin da Barcelona ta yi shekaru 9 da suka wuce ya jefa Neymar da Ubansa a matsala

Cinikin da Barcelona ta yi shekaru 9 da suka wuce ya jefa Neymar da Ubansa a matsala

  • ‘Dan wasan gaban kungiyar PSG, Neymar Jr. zai je kotu a kan tashinsa daga Santos a 2013
  • Wata kungiya a Brazil ta shigar da kara, tace an boye gaskiyar cinikin da aka yi da Barcelona
  • Neymar, Mahaifinsa da Shugabannin Barcelona Bartomeu da Sandro Rosell suna cikin matsala

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Spain - ‘Dan wasan kasar Brazil watau Neymar Jr. zai je kotu a watan Oktoban 2022, inda za ayi shari’a da shi a dalilin zuwansa kungiyar Barcelona.

Marca ta kawo rahoto a ranar Laraba 27 ga watan Yuli 2022 cewa za ayi shari’a da ‘dan wasan da iyayensa da wasu tsofaffin shugabannin kulob din.

Sandro Rosell da Josep Maria Bartomeu za su amsa tambaya a game da cinikin tauraron da aka yi daga kungiyar Santos zuwa Barcelona tun a 2013.

Kara karanta wannan

NNPC yayi karin-haske kan batun korar Ma’aikata 500 tun da kamfani ya canza tsari

Wata majiya tace ana zargin an aikata ba dai-dai ba wajen wannan ciniki, don haka ake tuhumar Rosell da kuma Bartomeu da laifin satar kudin kulob.

Tsofaffin shugabannin kungiyar ta Sifen za su shiga kotu ne daga 17 zuwa 31 ga watan Oktoba.

Neymar ya tafi PSG

Daga baya Neymar Jr. ya bar kungiyar ta Sifen, ya koma Faransa bayan Paris Saint-Germain ta saye shi a kan kudi fam miliyan €222 a kakar 2017.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Neymar da Ubansa
'Dan wasan PSG, Neymar da Mahaifinsa Hoto: www.marca.com
Asali: UGC

Sai dai abin mamakin shi ne tashinsa daga Barcelona wanda ya girigiza Duniya a lokacin bai jawo shari’a a kotu ba, sai barinsa kasarsa da ya yi.

DIS ta shigar da kara

Abin da ya faru shi ne wata kungiya a kasar Brazil mai suna DIS ta shigar da kara a kotu. DIS ta taba zama cikin masu hakki kan ‘dan kwallon kafan.

Kara karanta wannan

2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

Da farko Barcelona ta fadawa Duniya cewa a kan €57.1m ta saye Neymar daga Santos, iyayensa suka tashi da €40m, sai kungiyar Santos ta karbi €17.1m.

Daga baya Lauyoyi sun gano kudin da aka kashe wajen cinikin ya zarce €80m. Mirror tace dalilin haka Bartomeu da Sandro Rosell suka samu matsala.

DIS wanda aka biya €6.8 a cikin kudin da aka ba Santos, ta na zargin Neymar da Barcelona sun boye hakikanin kudin da aka kashe wajen cinikin.

Ronaldo ya yi kwantai?

A kwanakin baya kun ji labari cewa akwai jita-jitan Cristiano Ronaldo yana neman kai da Manchester United ko kungiyar yana neman kai da shi.

Jorge Mendes wanda shi ne dillalin Ronaldo, ya dage wajen samun masu sayen ‘dan wasansa, amma dai har zuwa yanzu ciniki bai fada da kowa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel