Anthony Joshua Bai Samu Yadda Ya So Ba, Ya Fusata da Usyk Ya Doke Shi a Dambe

Anthony Joshua Bai Samu Yadda Ya So Ba, Ya Fusata da Usyk Ya Doke Shi a Dambe

  • A wasan damben da aka yi a Birnin Jeddah da ke kasar Saudi Arabia, Oleksandr Usyk ya kuma doke Anthony Joshua
  • Joshua wanda ‘Dan asalin Najeriya ne ya gagara karbe kambunsa daga hannun gwarzon WBA, IBF, WBO da kuma IBO
  • Yanzu an fara maganar Tyson Fury ya dawo su buga da Oleksandr Usyk, ganin ‘Dan kasar Ukraine din ya gagari Duniya

Saudi Arabia - Shahararre kuma gwarzon ‘dan dambe nan watau Anthony Joshua, ya gagara karbe kambun Duniya daga hannun Oleksandr Usyk.

Rahotanni daga Sky Sports sun tabbatar da cewa Oleksandr Usyk ne ya kuma samun galaba a kan mutumin Najeriyan da aka haifa a kasar Birtaniya.

Wannan dambe da aka yi a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta 2022, ya yi zafi domin sai da aka kai zagaye na 12 ana bugawa kafin a samu gwarzo.

Kara karanta wannan

Daliban Jami’a Sun Ki Daukar Shawarar Minista, Za Su Kai Gwamnati kotu kan ASUU

‘Dan damben na kasar Ukraine ya yi galaba bayan Alkalai sun ba shi nasara. Hukuncin da Alkalai suka yi shi ne: 113-115, 116-112 sau 115-113.

Wannan ne karo na biyu a jere da Oleksandr Usyk ya doke Anthony Joshua mai shekara 32 a Duniya, kwanakin baya ya doke shi a garin Landan.

Joshua ya yi bakin kokarinsa

Jaridar Marca ta rahoto cewa Anthony Joshua ya yi kokari kwarai da gaske a damben, fiye da yadda ta kaya a lokacin haduwarsu na baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Anthony Joshua
Oleksandr Usyk da Anthony Joshua Hoto: talksport.com
Asali: UGC

Har zuwa zagaye na tara, Anthony Joshua ne ake tunanin zai yi nasara a kan abokin damben na sa, amma a karshe Usyk ne ya samu kai labari a jiya.

Joshua ya yi ta kokarin gwabje Usyk da naushi a inda za iyi masa illa a jikinsa, da aka isa zuwa zagaye na goma, sai tsohon gwarzon ya fara gajiya.

Kara karanta wannan

Adamawa: Kotu Ta Umurci A Rataye Shahararen Ɗan Damben Gargajiya Na Najerya Har Sai Ya Dena Numfashi Saboda Kashe Matarsa Da Mugun Duka

Rahoton yace a zagaye uku na karshe da suka rage Usyk ya nunawa kowa shi gwarzon Duniya ne.

AJ bai ji shawara ba

Kafin ayi wannan wasa, Tyson Fury ya gargadi Anthony Joshua a kan irin kuskuren da manyan ‘yan wasan dambe irinsu Deontay Wilder suka yi a baya.

A karshe dai Joshua bai samu damar karbe kambunsa daga hannun Oleksandr Usyk ba, a wasan aka sallamawa ‘dan damben cewa lallai ya kai gwarzo.

Anthony Joshua bai iya boye fushinsa ba, ya jefar da kambu biyu bayan an doke shi. Ana tunanin za iyi wahala ya sake lashe su idan har Usyk na wasa.

FIFA ta dakatar da Indiya

A fagen kwallon kafa, ku na da labari FIFA ta dakatar da AIFF saboda an samu kotu ta tsoma baki a kan shugabancin kungiyar wasan kwallon Indiyar.

A dalilin wannan, zai yi wahala a bar kasar Ingila ta dauki nauyin gasar U-17 na mata da za ayi a shekarar nan 2022, watakila dole a tafi wata kasar.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Mutumi Ɗauke Da Bindigu Zai Kai Su Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel