Daliban Jami’a Sun Jefar da Shawarar Minista, Za Su Kai Gwamnati kotu kan ASUU

Daliban Jami’a Sun Jefar da Shawarar Minista, Za Su Kai Gwamnati kotu kan ASUU

  • Malam Adamu Adamu ya zuga daliban Najeriya su kai karar kungiyar ASUU zuwa kotu saboda yajin-aikin da ake yi a jami’o’i har yau
  • Shugaban Kungiyar dalibai na kasar nan, Sunday Ashefon maidawa Ministan ilmin martani cewa gwamnatin Najeriya ya dace a kai kotu
  • Sunday Ashefon ya bayyana cewa ba za a zargi ASUU da yin yajin-aiki ba, said ai Gwamnatin da ta gagara bunkasa harkar ilmin Najeriya

Abuja - Kungiyar dalibai na kasar nan baki daya watau NANS, tace ta soma tattaunawa domin shigar da karar gwamnatin tarayya a kotu.

Punch ta ce a ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta 2022, kungiyar ta NANS ta shaida mata cewa ta na kokarin yin shari’a da gwamnati da Ministan ilmi.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

NANS tafitar da wani jawabi na musamman ga ‘yan jarida a garin Abuja, bayan Malam Adamu Adamu ya yi kira ga dalibai suyi karar malamansu.

Shugaban NANS na kasa, Sunday Ashefon ya maidawa Ministan ilmin martani da cewa gwamnatinsa za a maka a kotu ba 'yan kungiyar ASUU ba.

Yau Adamu Adamu ya fadi gaskiya - NANS

“Abin da Adamu Adamu ya taba dacewa a kai tun da ya zama Minista shi ne cewa da ya yi akwai bukatar a biya dalibai bata masu lokaci, dama da dukiya da aka yi.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Amma kuma Ministan ya nemi ya yi wa kansa wayau da ya bada shawarar ASUU za ta biya asarar da aka yi. ASUU ba ta da hannu, kuma ba ta amfana da kudin jami’a.”
Buhari WASCCE
Buhari ya karbi shaidar WAEC Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Raina tunani ne a kawo maganar cewa dalibai su kai karar ma’aikata saboda sun koka a kan mummunan halin aiki da suke ciki, a maimakon wadanda suka dauke su aikin.”

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

- Sunday Ashefon

Sunday Ashefon: Ina laifin ASUU?

Kamar yadda aka kawo rahoto a Blueprint, Sunday Ashefon yace gwamnatin tarayya ce ke cin moriyar kudin da ake biya a jami’o’i ba ASUU ba.

Rahoton yace Kwamred Ashefon yace NANS za ta yi amfani da shawarar Ministan ilmi, ta shiga kotu domin neman a biya su diyyar bata masu lokaci.

Shugaban na ASUU yace sun yi asarar lokacinsu har abada, amma za a iya yin wani abin a kan kudin gidaje da irinsu lokacin zuwa NYSC da suka bata.

A karshe, daliban kasar sun yi kira ga gwamnatin tarayya, da ta yi duk abin da za ta iya wajen shawo kan kungiyar ASUU, domin malamai su koma aji.

Babu aiki - babu kudin aiki

An ji labari Ministan ilmi, Malam Adamu Adamu yace babu yadda za ayi gwamnati ta dauki kudi, ta biya malaman da ba su yi aikinsu na koyar da dalibai ba.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Na Tambayi Peter Obi a Zaman da Nayi da Shi inji Sheikh Ahmad Gumi

Amma malaman Jami’an kasar sun ce ba za a bude makarantun gwamnati ba sai an biya su duka kudin wata da watannin da suka dauka su na yin yajin-aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel