Yaron da Budurwar Ronaldo ta haifa ya koma, ‘Dan wasan Man Utd ya yi hadarin mota

Yaron da Budurwar Ronaldo ta haifa ya koma, ‘Dan wasan Man Utd ya yi hadarin mota

  • Daya daga cikin jariran da Budurwar Cristiano Ronaldo watau Georgina Rodriguez ta haifa, ya mutu
  • Cristiano Ronaldo ya sanar da wannan a Instagram, ya bukaci mutane su ba su dama su wartsake
  • Kocin Man Utd ya ce Bruno Ferndades ya yi hadarin mota a kan hanyarsa ta zuwa filin wasa a jiya

Manchester - A ranar Litinin, 18 ga watan Afrilu 2022 ne fitaccen ‘dan wasa, Cristiano Ronaldo ya bada sanarwar cewa jaririn da suka haifa ya koma.

Cristiano Ronaldo ya fito shafinsa na Instagram ya bayyana cewa yaron da suka samu ya rasu a lokacin da Georgina Rodriguez ta je haihuwar tagwaye.

Goal.com ta ce an sa ran Rodriguez za ta haifi ‘yan biyu, amma sai aka tashi da mummunan labari a jiyan na cewa daya daga cikin jariran bai yi rai ba.

Kara karanta wannan

An gano abu 1 da ya hana a fito da Dariye, Nyame daga gidan yari tun da an yafe masu

Sai dai Rodriguez mai shekara 28 tayi nasarar haihuwar macen da ke cikin ta. Kawo yanzu ba a san wani suna aka radawa jaririyar da aka samu ba.

Da yake bayani, ‘dan wasan na Manchester United ya bukaci a kyale su, su ji da makokin rashin, ya godewa malaman asibitin da suka karbi haihuwar.

‘Dan wasan gaban ya na da wasu yaran; Cristiano Jr da Mateo, sai kuma ‘yan mata Eva Da Alana.

Budurwar Ronaldo
Ronaldo da iyalinsa Hoto: www.dailymail.co.uk
Asali: UGC

Jawabin Ronaldo

“Mu na masu tsananin takaicin bada sanarwar jaririnmu ya mutu. Mun ji duk zafin da iyaye za su iya ji.”
“Haihuwar jaririyar ne kurum ya ba mu kwari da farin ciki a yanzu. Mu na so mu godewa likitoci da malaman jinya da kwarewarsu da taimakonsu.”

-Cristiano Ronaldo

Kara karanta wannan

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun hallaka wani adadi mai yawa

Bruno Fernandes ya yi hadari

A gefe guda kuma, Bruno Fernandes ya gamu da hadarin mota duk a cikin farkon wannan makon.

Daily Mail ta ce an yi dace ‘dan wasan tsakiyan na Manchester United bai gamu da wani rauni ba a lokacin da kungiyarsa ke shirin buga babban wasa da Liverpool.

‘Dan wasan ya na tuka wata motarsa Porsche ne a yayin da ya gamu da wannan hadari. An tabbatar da cewa babu wanda ya samu rauni a sanadiyyar abin da ya faru.

Ralf Rangnick ya ce shakka babu ‘dan wasan ya yi hadari ne a hanyar zuwa filin horaswa na Carrington, kuma a iyaka saninsa Fernandez zai buga wasan yau.

Rodriguez ta na samun miliyoyi duk wata

A baya kun ji yadda Budurwar da ake sa rai Cristiano Ronaldo zai aura watau Georgina Rodriguez ta ke wanke biyar, ta tsoma goma, alhali ta taso ne a marainiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga ASUU: Ku yi hakuri ku koma aji ku ci gaba da karantarwa

Kusan duk wata, Miss Georgina Rodriguez ta na iya samun kudin da ya kai Naira miliyan 50 a asusun ta. Masoyin na ta ya ware mata kudi domin kula da yara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel