Cristiano Ronaldo ya daura Budurwarsa a kan albashi, ta na samun N45m duk wata

Cristiano Ronaldo ya daura Budurwarsa a kan albashi, ta na samun N45m duk wata

  • Budurwar da ake sa rai Cristiano Ronaldo zai aura, Georgina Rodriguez ta na wanke biyar, ta tsoma goma
  • Kusan duk wata, Miss Georgina Rodriguez ta na iya samun kudin da ya kai Naira miliyan 50 a asusun ta
  • ‘Dan wasan na kungiyar Manchester United ya kan turawa uwar ‘ya ‘yansa makudan kudi na kula da gida

England - ‘Dan wasan gaban kungiyar Manchester United, Cristiano Ronaldo, ya na biyan buduwarsa fiye da €100,000 a kowane watan Duniyan nan.

Wani rahoto daga El Nacional ya bayyana cewa ‘dan wasan ya na biyan Georgina Rodriguez wadannan kudi saboda irin dawainiyar da ta ke yi wa iyali.

Kamar yadda jaridar Marca ta kawo rahoto, Cristiano Ronaldo da sahibarsa watau Georgina Rodriguez su na cikin shahararrun masoya a Duniyar yau.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dakile mota dauke da N100m kudin fansa za'a kaiwa yan bindiga

Ronaldo da kuma Rodriguez su na samun makudan kudi a duk shekara daga tallace-tallace da suke yi wa kamfanoni a shafukan sada zumunta na zamani.

A wani shiri da ake yi a gidajen talabijin na kasar Sifen mai suna 'Viva La Vida', an rahoto cewa a kowane wata, Ronaldo ya kan aikawa sahibarsa kudi a banki.

N50m domin dawainiya iyali

Ana tunanin kudin da ‘dan kwallon kafan ya kan tura cikin asusun budurwar ta sa ya kai €100,000. A lissafinmu na Naira, wannan kudi sun kusa N50m.

Cristiano Ronaldo da Budurwarsa
Cristiano Ronaldo zai auri Georgina Rodriguez Hoto: www.world-today-news.com
Asali: UGC

Amfanin wannan kudi shi ne tayi hidimar gabanta da kuma dawainiyar yara. Georgina mai shekara 28 ce ta ke kula da ‘ya ‘yan babban ‘dan wasan Duniyan.

Sahibar Ronaldo ta yi kudi

A wani bidiyo da aka fitar a kan tarihin wannan Baiwar Allah a kafar Netflix, ta nuna yadda ta ke hada hidimar iyali da kuma kasuwanci da sauran neman kudi.

Kara karanta wannan

Damfara: An kama 'yar shekara 24 da ta addabi Kanawa da sata da katunan ATM

Georgina Rodriguez ta na tashi da kimanin fam €8,000 a kowane wata daga tallan da ta ke yi. Bayan nan kuma ta na da wasu hanyoyin samun kudin shiga.

Georgina Rodriguez ta guji dangi

A shirin na 'Viva La Vida', an zargi Georgina da kin kula da ‘yanuwanta. Kwanakin baya da kakarta ta mutu a kauyen Jara, ana zargin ba ta je jana’izar ba.

Wani baffanta, Jesus Hernandez ya yi tir da halin ta bayan shi ya rika kula da su a lokacin su na kanana. A cewarsa, yanzu ta samu daula, ta na kyamar dangi.

Alherin Ronaldo, Neymar Ozil, dsr

Baya ga buga kwallon kafa, akwai wasu ‘yan wasa da suka yi suna wajen yin kyauta da alheri. Kamar yadda mu ka kawo maku rahoto, daga ciki akwai Ronaldo.

Ronaldo yana cikin ‘yan kwallon da suka yi fice wajen kyauta, hakan ta sa ya taba lashe kyautar “Athletes Gone Good Award”, ya taba kyautar $83,000 a lokaci daya.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur za ta zama tarihi, Lai ya nuna yadda matatar Dangote za ta taimaki Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel