An gano abu 1 da ya hana a fito da Dariye, Nyame daga gidan yari tun da an yafe masu

An gano abu 1 da ya hana a fito da Dariye, Nyame daga gidan yari tun da an yafe masu

  • A makon da ya wuce ne gwamnatin Najeriya ta yi afuwa ga wasu mutane 150 da ke tsare a gidan yari
  • Sanannu daga cikin wadanda aka yafewa laifuffukan da suka aikata su ne Joshua Dariye da Jolly Nyame
  • Abin da ake jira kafin a saki su Joshua Dariye da Jolly Nyame shi ne Ministan shari’a ya aiko da takarda

Abuja - Kwanaki biyar kenan da majalisar kolin Najeriya ta yi afuwa ga wasu mutane 159 da aka samu da laifi, amma har yanzu ba su samu ‘yanci ba.

Wani rahoto da ya fito daga Punch a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu 2022 ya bayyana cewa Joshua Dariye da Jolly Nyame su na tsare har yanzu.

Tsofaffin gwamnonin na jihohin Taraba da Filato ba za su fito daga gidan gyaran hali ba, har sai Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya sa hannu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

Akwai bukatar babban lauyan gwamnatin tarayyar ya rubuta takarda zuwa ga gidajen yarin da wadannan manyan mutane su ke, kafin a iya fito da su.

Da zarar takardar Ministan ta shiga hannun hukumar kula da gidajen yarin, za a saki ‘yan siyasar kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yi masu afuwa.

Humphrey Chukwuedo ya yi magana

Mai magana da yawun gidajen yari da ke Abuja, Humphrey Chukwuedo, ya shaidawa manema labarai cewa takardar Ministan shari’a kurum suke jira.

Abubakar Malami
AGF Abubakar Malami SAN Hoto: @MalamiSAN
Asali: Facebook

“Yanzu haka ina gidan gyaran hali na Kuje, kuma har yanzu ba mu samu takarda daga AGF ba. Da zarar an samu takardun, za a fito da su.”
Ba mu da dalilin cigaba da tsare su muddin AGF ya ba mu umarni. Ba a kawo mana takarda ba. A dalilin haka, har yanzu, su na hannunmu.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

- Humphrey Chukwuedo

Shari’ar Dariye da Nyame

Alkali mai shari’a Adebukola Banjoko ne ya kama wadannan ‘yan siyasa da laifin satar dukiyar al’ummarsu a lokacin da suke rike da kujerun gwamnoni.

An yankewa Rabaren Nyame wanda ya yi gwamna sau uku hukuncin daurin shekaru 12 a gidan maza. Haka aka tabbatar da wannan dauri har kotun koli.

Amma kotun daukaka kara ta rage hukuncin Sanata Dariye zuwa shekaru 10 a gidan yari. Alkalan kotun kolin Najeriya sun kuma tabbatar da wannan daurin.

An bar EFCC da ICPC da kumfar baki

Rahoto ya nuna cewa ma’aikatan da suka saida ransu a EFCC da ICPC sun yi tir da yafewa Jolly Nyame da Joshua Dariye, su ka ce an maida su abin dariya.

Bayan tsawon shekara da shekaru ana shari'a, Muhammadu Buhari ya yi wa wadanda aka samu da laifi afuwa, duk da yana ikirarin yaki da rashin gaskiya.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Asali: Legit.ng

Online view pixel