Manchester United ta fita daga batun Zidane da Pochettino, ta na shirin nada sabon koci

Manchester United ta fita daga batun Zidane da Pochettino, ta na shirin nada sabon koci

  • Watakila Manchester United ta nada Ralf Rangnick a kan kujerar da Ole Gunnar Solskjaer ya bari
  • Kungiyar Ingilar ta ajiye magana da Lokomotiv Moscow a kan daukar Rangnick mai shekara 63
  • Ralf Rangnick ya horar da kungiyoyi irinsu Schalke, Hoffeinham, da kuma RB Leipzig a kasar Jamus

England - Manchester United na shirin nada Ralf Rangnick a matsayin kocin wucin gadi. Kungiyar kwallon kafan za ta ba kocin kwantiragin wata shida.

BBC ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, 2021, tace kungiyar Man United ta cin ma yarjejeniya da Lokomotiv Moscow a game da Rangnick.

A halin yanzu Ralf Rangnick shi ne shugaban sashen cigaban wasan kwallon kafa a kungiyar ta Moscow.

Rahotanni sun ce Bajamusen kocin ne zai maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer wanda aka sallama bayan ya yi shekara uku ba tare da ya iya lashe wani kofi ba.

Kara karanta wannan

'Kuncin rayuwa ta tunzura ni: Matashin da aka kama da hodar iblisa ta N2.7bn a filin jirgin Abuja

Abin da ya rage shi ne Rangnick ya samu takardar yin aiki a Birtaniya. Daga nan sai a saurari kungiyar kwallon kafan ta bada sanarwar kawo sabon koci.

Manchester United
Ralf Rangnick Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanene Ralf Rangnick?

Tun a shekarar 1983, Rangnick ya fara aikin horas da ‘yan kwallo. A wancan lokaci kocin mai shekara 63 a yanzu ya na matashi ‘dan shekara 25 rak.

A 2011 ne Rangnick ya lashe gasar German Cup da kungiyar Schalke 04. Baya ga haka ya kai kungiyar RB Leipzig zuwa wasan karshe na gasar a 2019.

Da yake aikin koci a kasar Jamus, Rangnick ya jagoranci kungiyar Schalke zuwa wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai a kakar 2010/11.

Sky Sports tace ana yi wa kocin kallon Farfesa a Jamus, domin ya san harkar horar da ‘yan wasa. Rangnick ya fito da koci da ‘yan wasa da dama a Turai.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Sojoji sun kame wani babban jami'an IPOB, sun kwato makamai

A shafinsa na Twitter, ‘dan jaridar nan, Fabrizio Romano ya tabbatar da rahotannin da ke yawo a kan nadin tsohon mai horas da Schalke 04 da Leipzig.

Zidane ba zai zo Old trafford ba?

Mun kawo maku rahoto cewa an sallami Ole Gunnar Solskjaer daga aikin horas da ‘yan wasan kungiyar Manchester United a karshe makon da ya wuce.

Zinedine Zidane yana cikin wadanda ake rade-radin zuwansu kungiyar Manchester. Haka zalika ana tunanin kawo Erik ten Hag ko Mauricio Pochettino.

Asali: Legit.ng

Online view pixel