Yanzu-yanzu: Sojoji sun kame wani babban jami'in IPOB, sun kwato makamai

Yanzu-yanzu: Sojoji sun kame wani babban jami'in IPOB, sun kwato makamai

  • Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wani Obinna Nwite, wanda ta ce sakataren haramtacciyar kungiyar IPOB ne
  • An kama Nwite da makamai da alburusai da kuma rajista mai dauke da sunayen mambobin kungiyar ta IPOB
  • Rundunar sojin ta ce tuni aka mika jami’in na kungiyar ta IPOB ga hukumomin domin fuskantar shari’a

Najeriya - Rundunar sojin Najeriya a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba ta bayyana cewa ta kama sakataren kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Obinna Nwite.

Mukaddashin daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Birgediya-Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba.

Sojojin Najeriya
Yanzu-yanzu: Sojoji sun kame wani babban jami'an IPOB, sun kwato makamai | Hoto: Defence Headquarters
Asali: UGC

Birgediya-Janar Onyeuko ya ce:

“Ayyukan IPOB/ESN a kudu maso gabas sun ragu matuka a ‘yan kwanakin nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

“Duk da haka, an samu faruwar wasu abubuwa a wasu wurare a; karamar hukumar Oru-West ta jihar Imo da karamar hukumar Ebonyi ta jihar Ebonyi.

Onyeuko ya ce sojojin sun amsa kiraye-kirayen da aka yi musu tare da kai samame a wasu yankunan IPOB a cikin 'yan kwanakin nan.

Abubuwan da sojoji suka kwato

Ya kara da cewa:

“A wasu daga cikin wadannan ayyuka, sojoji sun kama daya daga cikin sakatarorin kungiyar ta IPOB, Mista Obinna Nwite, tare da kwato kananan bindigogi guda hudu, dogayen bindigogi guda uku, alburusai iri-iri 18 da kuma littafin daukar bayanan taro, dauke da wasu sunayen ‘yan kungiyar ta IPOB.
“’Yan ta’addar IPOB/ESN da aka kama da duk wasu kayayyakin da aka kwato an mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki na gaba.

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

Jami’an tsaro na hadin gwiwa a ranar Talata sun yi artabu da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne a garin Ihiala na jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

Yankin karamar hukumar da ake gudanar da zaben na gwamna ya yi kaurin suna wajen tabarbarewar tsaro, wanda ya kai ga sauya zabe a yankin.

Artabun wanda ya gudana a mahadar Mbosi Osumowu da ke kan iyakar Anambra ya shafe kusan awanni uku ana yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel