Jihar Sokoto
Yan fashin daji sun kai hari tare da garkuwa da sarkin Gobir Isa Bawa da ɗansa a hanyarsu ta komawa gida a ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato.
Sheikh Bello Yabo ya bayyana matsayarsa kan zanga-zanga inda ya ce shi bai ce a yi ko kada a yi ba inda ya shawarci malamai kan shiga lamarin zanga-zanga.
Minsitan Tinubu ya ce bai kamata 'yan Najeriya su fara kuka kan halin da ake ciki a kasar nan ba, inda yace ya kamata a kara hakuri zuwa wani lokaci a gani.
Ministan albarkatun ruwa, Muhammad Goronyo ya bukaci 'yan Najeriya da kada su shiga cikin zanga-zangar da ake shirin yi domin adawa da gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa babu ruwanta da zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a fadin kasar nan. Ta ce zanga-zangar ba ta da amfani.
Wani matashi mazaunin jihar Sokoto, Buhari Haruna ya nemi daukin jama'a kan gano wanda ya sace masa injin hada-hadar kudi na POS har wurin sana'arsa.
Hukumar SEMA a jihar SOkoto ta tabbatar da rasa gidaje 1,664 sakamakon mamakon ruwan sama da ya samar da ambaliyar ruwa a wasu garuruwan dake jihar.
Malamin Musulunci a jihar Sokoto, Murtala Bello Asada ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu da masu kushe zanga-zanga tare da kiran kawo karshen mulkinsa.
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zabe ta bayyana zaben dan majalisar tarayya na Yabi da Shagari a matsayin wanda bai kammalu ba, ta umarci INEC ta ƙarisa zaɓe.
Jihar Sokoto
Samu kari